BBC Hausa of Monday, 17 July 2023

Source: BBC

‘Yadda muka maƙale a tsakiyar teku bayan man jirgi ya ƙare’

Wasu mutane da suka tsira daga nutse wa Wasu mutane da suka tsira daga nutse wa

"Mun kai wajen mutane 140 da muka hau jirgin ruwa a gabar tekun da tsakar dare, da misalin karfe 2 na safe."

Doudou Diop, mai shekaru 30 daga kasar Senegal, ya yi kasadar komai a kan tafiya a hatsarin gaske a cikin wani kwale-kwale zuwa Turai, inda yayi tafiyar kilomita 1,700 daga Senegal zuwa tsibirin Canary na Spain.

Wannan hanya ta tekun Atlantika ta kasance cikin labarai bayan wata kungiya me zaman kanta ta ce wasu jiragen ruwa guda uku dauke da mutane akalla 300 sun bace tun karshen watan Yuni.

Nayi tafiya zuwa kauyen kamun kifi mai nisa da ake kira Kafountine a kudancin Senengal, inda daga nan ake fara tafiya don yin bincike.

Wuri ne da daruruwan mutane ke tashi ko wace shekara don neman ingantaciyar rayuwa a Turai.

Na ci karo da Doudou Diop yana zaune a bakin barandar gidansa a cikin ruwan sama da tsawa, dukan matan danginsa sun taru a kusa da shi.

"Mun tashi ba tare da wata matsala ba kuma mun yi nasarar zuwa Morocco," in ji shi.

"Muna da nisan kilomita 500 daga tsibirin Canary sai kwatsam injinmu ya tsaya. Man fetur ya kare kuma muka makale a tsakiyar teku inda muka kasa ci gaba."

Ya ce hukumomin kasar Moroko sun dauko dukkan su 140 tare da kai su birnin Nouadhibou mai tashar jiragen ruwa mafi kusa da kasar Mauritania.

"Sun dauki sunayenmu da shaidarmu kuma suka sanya mu a cikin motocin da za su komar da mu gida a Senegal."

Anyi Sati daya da bacewarsa saboda haka danginsa sun ji dadin dawowar sa da ran sa.

Babu tabbas ko an ambaci jirgin ruwan da yake ciki a cikin wata sanarwa ko sanarwar manema labarai.

A halin da ake ciki kuma, takaddama ta barke tsakanin gwamnatin Senegal da wata kungiyar 'yan gudun hijira da ake kira 'Walking Borders' game da bakin haure nawa aka yi hasarar a teku.

Batun ya shiga kafafun yada labarai

Wace ta kafa kungiyar 'Walking Borders', Helena Maleno, ta fara ankarar da mutane a ranar 9 ga Yuli.

Ta ce ta tuntubi hukumomi a Senegal, Mauritania, Morocco da Spain, inda ta bukace su da su shiga aikin neman jiragen ruwan da suka bata.

Hukumomin kasar Spain sun ceto bakin haure 86 daga cikin kwale-kwalen da ya taso daga tsibirin Canary a lokacin da suke aikin neman daya daga cikin 'yan kwale-kwalen da suka bata.

Daga nan ne ma'aikatar harkokin wajen Senegal ta fitar da sanarwa.

"Binciken da aka gudanar ya nuna cewa wadannan bayanan ba su da tushe," in ji ta, ta kara da cewa an ceto 'yan kasarta 260 a yankin ruwan Maroko tsakanin 28 ga watan Yuni zuwa 9 ga Yuli.

Daga nan ne kungiyar Walking Borders ta fitar da wani karin bayani, inda ta ce ta samu damar tabbatar da cewa wadanda aka ceto da gwamnatin Senegal ta ambata sun yi daidai da sauran jiragen ruwa "wadanda su ma suka bar gabar tekun Senegal amma ba kwale-kwalen da ke dauke da mutane 300 ba".

A ranar 13 ga watan Yuli, wani jirgin ruwa dauke da bakin haure 41 da suka tashi daga kasar Senegal ya sauka a tsibirin Canary.

Yayin da nake kokarin tattara bayanai na, na sami mace guda a cikin Kafountine wadda ta ce tana da wani dangi da ya ɓace. Ta so kar a bayana sunanta kuma ta gaya mani cewa ta daina jin duriyar yar'uwanta dan shekara 17.

Da alama yana cikin ɗaya daga cikin waɗannan jiragen ruwa uku, "Ina jin tsoro, ba mu da wani labari game da shi," in ji ta. "An yi kwanaki."

Wani ma’aikacin jami’an tsaron yankin da bai son shima a bayyana sunansa ya shaida mani cewa, “Akwai matukar rudani game da bacewar mutane 300”.

Jami’in ya kara da cewa, “Baya ga wannan matar, a nan garin babu wanda ya kai wa hukuma ko jami’an tsaro cewa suna neman ‘yan uwansu ko ‘yan uwansu.

Amma wannan ba abin mamaki bane saboda mutane da yawa sun fito daga wasu yankuna ko ma makwabta ne, kuma ba su da alaƙa da ƙauyen.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya, akalla mutane 559 ne suka rasa rayukansu a shekarar da ta gabata a kokarinsu na isa tsibirin Canary daga Senegal.

Kuma a farkon rabin wannan shekara kadai, tsibirin Canary sun karbi bakin haure fiye da 7,000.

Mafarkina bai zama gaskiya ba

Yanayin tattalin arziki mai tsauri yana nufin koyaushe akwai tarin mutane masu neman damar samun ingantacciyar rayuwa.

Doudou ya rayu a yankin kudancin Casamance na Senegal duk tsawon rayuwarsa. Bayan mutuwar mahaifinsa, ya ce ya ji matsin lamba don ya yi wa iyalinsa tanadi a matsayin ɗan fari.

"Ina da burin samun ingantacciyar rayuwa, ingantacciyar kuɗi don in kula da matata da 'yata, mahaifiyata da sauran dangi na," in ji shi, ya kara da cewa kujera a cikin kwale-kwalen ya kai CFA 400,000 ($ 682).

“Na tafi ba tare da na sanar da kowa ba, na yi shirin tafiya Turai ne saboda babu komai a nan, ba ni da komai."

"Na ji takaici saboda ina son zuwa Spain, ina da abokai da suke can kuma suna jirana."

A tsakiyar Kafountine, akwai gungun matasa zaune a cikin inuwa. Wasu na yin wasannin allo na gargajiya yayin da wasu kuma ke ta ce-ce-ku-ce kan siyasa.

Gnara Diabang Ba, tana daya daga cikin mataimakan magajin gari, kuma 'yar jam'iyyar adawa.

“A gaskiya abin ya dame ni, abin bakin ciki ne ganin yadda muka shahara saboda bakin haure da ke tashi zuwa Turai ko kuma kokarin tafiya Turai.

"A matsayina na zababbiyar jami'ar karamar hukuma, ina jin nauyin da ya rataya a wuyanmu, idan muka ce matasa su zauna, dole ne mu samar musu ayyukan yi, da ilimi mai kyau, idan ba mu yi haka ba, yana nufin mun gaza."

Magajin garin David Diatta ‘dan jam’iyya daya ne kuma ya yarda da ra’ayin ta, inda ya kara da cewa yanayin tsaro na musamman a yankin shi ma ya taka rawa.

"Abin da ke bayyana motsin ƙaura shine babban matsayi na gundumar Kafountine," in ji shi.

"Kashi 91 cikin 100 na al'ummarmu sun ƙunshi tsibirai kuma sojoji da na ruwa ba su da damar shiga yankin da abin da ke faruwa."

Rashin aikin yi na matasa ya kai kashi 40 cikin 100, hatta tsakanin wadanda suka kammala jami'a.

"Muna shan wahala a nan, babu ayyukan yi, babu taimako daga hukumomi," in ji Ibrahima 'dan shekara 28 da ya kammala karatun sociology a jami'a.

"Yawancin abokaina sun dauki kwale-kwalen kamun kifi don isa tsibirin Canary kuma sun yi nasara. Muna ganin su a shafukan sada labarai kuma hakan akwai bambanci.

"Da ace zan iya tafiya wata rana amma ina bukatar kudin."