BBC Hausa of Friday, 20 January 2023

Source: BBC

'Ƙungiyar ƙwadago na adawa da matakin CBN na taƙaita ƴancin kasuwanci a Najeriya'

Kwamared Ayuba Waba, Shugaban kungiyar ta NLC Kwamared Ayuba Waba, Shugaban kungiyar ta NLC

Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta ce ya kamata babban bankin kasar, CBN ya yi la’akari da halin da masu karamin karfi da mazauna yankunan karkara suke idan aka daina karbar tsofaffin takardun kudi daga ranar 31 ga watan Janairu kamar yadda bankin ya tsara.

Kungiyar ta yi kiran ne yayin da gwamnonon jihohin Najeriyar ke ganawa da gwamnan babban bankin kan wannan batu.

Shugaban kungiyar ta NLC ya ce wajibi ne bankin ya sake nazari kan matakin domin kauce wa mawuyacin halin da mazauna yankunan karkara za su iya shiga da kuma asarar da za su tafka.

Kwamared Ayuba Waba shi ne shugaban kungiyar ta kwadago, ya shaida wa BBC cewa sun hango matsaloli a cikin shirin na Babban Bankin na Najeriya.

"Ina ganin kamar ba a yi hangen nesa ba. Kashi 70 na tattalin arzikinmu ya kunshi kananan 'yan kasuwa ne."

Ya ce mutum irin wannan na iya tafiya kasuwa da kazarsa ko akuyarsa ya sayar a irin wadannan kasuwannin na karkara. Idan ma babu kudi a hannu, "masu sana'ar POS za su iya biyansa kudi ba tare da sai ya tafi banki ba."

Ya kuma ce ranar 20 ga watan Disamba kungiyar ta kwadago ta rubuta wa gwamnan babban bankin wasika, wadda a ciki ta bayyana damuwarta, musamman kan batutuwan da ya zayyana:

Na farko cikisnsu shi ne yawancin wurare ba su da bankuna ma samsam.

"Ina iya ba ka misali - a Jihar Borno inda na fito, cikin kananan hukumaomi 27 na jihar Kananan hukumomi uku ne kawai ke da rassan banki a cikinsu. Wadannan su ne Maiduguri da Jere da kuma Biu da hanyar Gombe."

Sai dai Mista Wabba ya ce duk da karin yawan kudin da babban bankin yayi, lamarin bai kai ga warware matsalolin ba.

"An sanar da mu cewa masu sana'ar POS su miliyan 18 ne a Najeriya. Duk inda ka je cikin karkara, sai da tsabar takardun kudi ake iya gudanar da kasuwanci."

Saboda haka ya ce idan ba a yi gyara ba, matsalar za ta fi shafan kananan 'yan kasuwa ne domin za ta hana su sarrafa kudaden da suke bukata domin yin kasuwanci.

Ya kuma bayyana cewa aniyar kungiyar kwadago ta kasar ita ce a sakar wa al'umma mara, musamman a karkara.

"Idan ranar 31 ga wannan watan 'yan Najeriya suka nuna rashin gamsuwa da matakin babban bankin Najeriya kan sauya tsofaffin takardun kudin da aka sake musu fasali zuwa sababbinsu, to ko shakka babu kungiyarmu ta kwadago za ta goyi bayansu," inji shi.