BBC Hausa of Thursday, 22 June 2023

Source: BBC

Ƙungiyoyi na gogayya kan Rice, Saudiyya ta ƙara janye ƴan Premier

Sandro Tonali Sandro Tonali

Newcastle United na dab da kammala cinikin dan wasan tsakiya na AC Milan Sandro Tonali, dan Italiya mai shekara 23 a kan fam miliyan 60. (Athletic)

Manchester United ta bi sahun Arsenal a zawarcin Declan Rice daga West Ham, inda United din ke duba yuwuwar sayenshi ta kuma hada har da Harry Maguire, ko Scott McTominay, ta bayar. (Telegraph)

Daman kuma West Ham tana son McTominay domin maye gurbin Rice din idan ya tafi. (Talksport)

Haka ita ma Manchester City ta shiga jerin masu gogayyar son Rice, amma kuma West Ham ta fi son cinikin da za a yi tsakaninta da City ya kasance ta samu har da Kalvin Phillips. (ESPN)

Shi kuwa Bernardo Silva ya kusa kammala yarjejeniyarsa ta barin City domin tafiya Saudi Arabia. (Marca)

A shirye Bayern Munich take ta bar Sadio Mane, ya bar kungiyar a bazaran nan inda Newcastle ke sha'awarsa. (Bild)

Haka kuma kungiyar ta Ingila tana son aron Ruben Neves, bayan da dan wasan na tsakiya na Portugal ya yarda ya je Al Hilal daga Wolverhampton Wanderers a kan fam miliyan 47 a wannan makon. (Football Insider)

Har yanzu Harry Kane, na da fatan cewa tafiyarsa zuwa Manchester United a bazaran nan za ta tabbata. (Mirror)

Kuma tuni Tottenham din ta cimma yarjejeniya ta baka kan sayen mai tsaron ragar Italiya Gugliemo Vicario a kan fam miliyan 17.2 daga kungiyar Empoli. (Sky Sports)

Manchester United da Bayern Munich su ne kan gaba a masu son sayen dan wasan gaba na Eintracht Frankfurt Randal Kolo Muani, na Faransa. (L'Equipe)

Haka kuma Red Devils din na duba yuwuwar sayen mai tsaron ragar Inter Milan, Andre Onana, dan Kamaru (Sky Sports Italy)

Bournemouth ta kusa kammala cinikin Justin Kluivert, dan Holland da Roma a kan fam miliyan 9.5 (Talksport)

Dan wasan tsakiya na Bayern Munich Ryan Gravenberch, na Holland mai shekara 21, ya ce yana son tafiya inda za a rika sa shi a wasa sosai, wanda hakan ya bude kofar tafiyarsa Liverpool. (Mirror)

Juventus ta yi wa dan wasanta na tsakiya Adrien Rabiot dan Faransa tayin sabon kwantiragi kafin na yanzu da zai kare a watan Yuli ya cika, amma kuma shi ya fi son tafiya gasar Premier, inda Manchester United da Newcastle ke sonshi. (Foot Mercado)

Dan wasan tsakiya na Italiya Jorginho, na son ci gaba da zama a Arsenal duk da cewa Lazio na sha'awarsa. (Evening Standard)

Shi kuwa Hakim Ziyech, na Chelsea, dan Morocco ya kusa kammala yarjejeniyar tafiya Al-Nassr ta Saudiyya a kan fam miliyan 8. (Standard)

Haka shi ma abokin wasansa a Chelsean Callum Hudson-Odoi, ka iya tafiya Saudiyyar inda kungiyoyi biyu suke sha'awar matashin na tawagar Ingila. (Athletic)