You are here: HomeAfricaBBC2023 05 19Article 1770221

BBC Hausa of Friday, 19 May 2023

Source: BBC

An dakatar da Klopp sakamakon kalaman da ya yi wa lafari

Kocin Liverpool Jurgen Klopp tare da wani lafari | Hoton alama Kocin Liverpool Jurgen Klopp tare da wani lafari | Hoton alama

An dakatar da Jurgen Klopp wasa biyu, sakamakon kalaman da ya yi wa alkalin wasa Paul Tierney.

Lamarin ya faru a lokacin wasan Premier League da Liverpool ta ci Tottenham 4-3 a cikin watan Afirilu.

Kenan Klopp ba zai ja ragamar Liverpool ba a fafatawar da za ta yi da Aston Villa a Anfield ranar Lahadi a gasar Premier.

An dage daya hukuncin wasa na biyu sai nan gaba, kenan kociyan zai ja ragamar kungiyar Anfield a karawar da za ta yi da Southampton.

Sai bayan kammala kakar nan za a sanar da ranar da Klopp zai yi zaman hukuncin dakatarwa karawa daya nan gaba.

Klopp ya fada cewar Tierney yana da ''wani kudiri mara kyau'' a kan Liverpool, bayan da aka tashi daga fafatawar.

An kuma ci tarar kociyan fam 75,000, bayan da ya tabbatar da yin kalaman da bai dace ba, ya kuma ce ya yi nadama da abubuwan da ya fada.

An bai wa Klopp katin gargadi, bayan da ya yi murnar cin kwallon da Liverpool ta yi a minti 94 a gaban alkalin wasa na hudu, inda dan Jamus ya ce abin da Tierney ya fada masa bai dace ba.

Klopp ya kuma rubuta wasikar bayar da hakuri da cewar kalaman da ya yi ba su dace ba.