You are here: HomeAfricaBBC2023 07 13Article 1803920

BBC Hausa of Thursday, 13 July 2023

Source: BBC

An naɗa Kanu a matsayin shugaban Enyimba

Nwankwo Kanu Nwankwo Kanu

An nada tsohon dan wasan Arsenal da Najeriya Nwankwo Kanu a matysayin shugaban kungiyar kwallon kafa ta Enyimba.

Gwamnan jihar Abia Alex Otti ne ya sanar da nadin.

Kanu ya karbi ragamar jagorancin daga Felix Anyansi-Agwu, wanda ya jagoranci kungiyar na tsawon shekaru 24 a lokacin da kungiyar ta lashe lambobin yabo da dama, ciki har da lashe gasar cin kofin CAF sau biyu.

Tsohon abokin wasan Kanu na Super Eagles, Finidi George, ya horas da ƙungiyar inda ya zama zakara a gasar lig na tara a bara da kuma samun gurbin shiga gasar cin kofin zakarun nahiyar Afrika ta CAF a kakar wasa mai zuwa.

Haka kuma an nada John Sam Obuh, wanda a kwanakin baya yana aiki da kungiyar Roma Academy da ke Abuja, a matsayin shugaban wata kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Abia Warriors.