You are here: HomeAfricaBBC2023 07 21Article 1809560

BBC Hausa of Friday, 21 July 2023

Source: BBC

Brighton ta yi watsi karo na biyu da Chelsea ta taya Caicedo

Moises Caicedo Moises Caicedo

Brighton ta yi watsi karo na biyu da Chelsea ta yi tayin fam miliyan 70, domin a sayar mata da Moises Caicedo.

Dan kasar Ecuador ya nemi izinin barin Brighton a cikin watan Janairu, bayan da Arsenal ta bukaci daukar dan kwallon.

Daga nan Brighton ba ta amince ya bar kungiyar ba, har ma ya saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da zama a kungiyar cikin watan Maris, wadda za ta karkare a 2027.

Kungiyoyi da dama daga masu buga Premier League sun yi zawarcin dan kwallon, sai dai Chelsea ce kan gaba a kokarin sayen dan wasan mai shekara 21.

Chelsea za ta kara da Brighton a wasan farko da aka hada gasa tsakanin masu buga Premier League shida da za a fara a Philadelphia daga ranar Asabar.

Caicedo zai je Amurka kai tsaye daga Ecuador, bayan dan hutu da yake yi, yayin da Brighton za ta bar Ingila zuwa Amurka ranar Talata.

Ya koma Brighton da taka leda daga Independiente del Valle ta Ecuador kan £4.5m a Fabrairun 2021, amma bai fara buga mata wasa ba a kakar.

Caicedo ya fara wasannin aro na rabin kakar 2021-22 a kungiyar Beerschot a Belgium daga baya Brighton ta bukace shi a Janairun 2022.

Ya fara buga Premier League a Afirilun 2022, wanda kawo yanzu ya yi karawa 53 da ci wa Brighton kwallo biyu.

Caicedo ya taka rawar gani da Brighton ta kare a mataki na shida a Premier League da ta wuce, wadda za ta buga Europa League a kaka mai zuwa.