You are here: HomeAfricaBBC2023 08 02Article 1817348

BBC Hausa of Wednesday, 2 August 2023

Source: BBC

Colwill ya tsawaita yarjejeniya shekara shida a Chelsea

Levi Colwill Levi Colwill

Mai tsaron baya, Levi Colwill ya sa hannu a kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda kaka shida bisa sharaɗin cewar za a iya tsawaita masa shekara ɗaya.

Ɗan ƙwallon tawagar Ingilan ya taimakawa Brighton wajen samun tikitin shiga Gasar Europa League a bara, inda ya buga mata wasannin aro 17 a Premier League.

Ɗan wasan mai shekara 20 ya yi ban-kwana da magoya bayan Brighton a shafinsa na sada zumunta ranar Talata.

Colwill ya shiga Chelsea yana da shekara takwas tun daga makarantar horar da tamaula ta ƙungiyar.

Ƙungiyar Stamford Bridge ta bayar da aron ɗan ƙwallon ga Huddersfield a 2021/22, wadda ya yi wa wasa 29 a Championship.

Bayan taka rawar gani a wasannin aro a Brighton, Colwill ya taimaka wa tawagar Ingila ta matasa 'yan shekara 21 wajen lashe kofin Turai karon farko a shekara 39.