You are here: HomeAfricaBBC2023 07 22Article 1809590

BBC Hausa of Saturday, 22 July 2023

Source: BBC

Dalilai uku da ke hana shugabannin jam'iyyu ɗorewa a Najeriya

Shuagabanin kungiyoyin siyaasa Shuagabanin kungiyoyin siyaasa

A Najeriya, masana siyasa na cigaba da tufa albarkacin bakinsu game da yadda manyan jam'iyyun siyasa suke sauya shugabanninsu ba tare da wa'adin mulkinsu ya kare ba.

A bayan nan APC mai mulki ta tabbatar da murabus din da shugabanta na kasa ya yi, wanda bai wuce shekara daya da `yan watanni ba daga cikin shekaru hudu na wa'adin mulkinsa.

Wasu masanan dai na danganta lamarin da rashin demokuradiyyar cikin jam`iyya da zargin mamayar da shugabanni daga bangaren zartarwa ke yi wa jam`iyya suna sarrafa ta yadda suke so.

Rashin nisan kwana ko karkon kifin da shugabannin jam'iyyun siyasa ke yi, wato daga ruwa sai wuta kamar yadda 'yan magana kan ce ya fara zama annoba a fagen siyasa a Najeriya.

Matsalar katse hanzarin shugabannin dai ba ta bar jam'iyya mai mulki ba, ballantana jam`iyyun hamayya.

Ko a ranar Litinin kwamitin gudanarwar jam'iyyar APC na kasa ya tabbatar da murabus din da shugaban jam'iyyar Sanata Abdullahi Adamu ya yi da sakataren jam'iyyar na kasa, Iyola Omishore.

A baya ma ba a yi rabuwar girma da arziki ba da shugabannin da suka gabace su ba, wato da Adams Oshiomhole da gwamnan Jihar Yobe, Alhaji Maimala Buni.

Ita ma jam'iyyar PDP da Labour da NNPP duka shugabanninsu na zubin baya-bayan nan ba su kai banten su ba.

Ko da a shekaru goma sha shida da jam`iyyar PDP ta yi tana mulkin Najeriya, kusan babu shugabanta da ya yi jagoranci ya sauka ana masa san barka.

Wasu ma sai da aka tabka shari'a. Ko da yake wasu sukan ce bisa radin kan su suka sauka.

Masana a fagen siyasa irin Farfesa Kamilu Fagge malami a jami'ar Bayero ta Kano da Dakta Abubakar Kari na Jami'ar Abuja sun bayyana wasu dalilai uku da suke ganin sune ummul aba'isin wannan matsala da ake fuskanta:

Ba dimokradiyya a jam’iyyu

Farfesa Kamilu Fagge ya bayyana wannan matsala a matsayin halin da jam'iyyu a Najeriya suka tsinci kansu ciki.

A mafi yawan lokuta "ɗauki ɗora ake yi" ko da kuwa shugabannin ba su cancanta ba, maimakon bai wa 'yan jam'iyya damar zaɓar mutumin da suke gani zai kai su ga nasara, tare da ɓullo da manufofi da za su kai jam'iyyar ga gaci.

Sharaɗin a mafi yawan lokuta shi ne biyawa tsirarin da suke iko da jam'iyyar muradansu a lokutan da aikin jam'iyyun ya taso.

Ko da yake Dr Kari ya ce ba wani baƙon abu ba ne wannan, musamman a irin lokutan da shugabannin jam'iyyar suka ƙi nuna goyon baya ga ɗan takarar da ya samu nasara.

"Idan shugaban jam'iyya ya ƙi goyon bayan Firaiminista ko shugban ƙasa lokacin yaƙin neman zaɓe ko a zaɓen fidda gwani, babu shakka bayan zaɓe dole ya ajiye muƙaminsa.

"Kowa ya sani Abdullahi Adamu bai yi Tinubu ba lokacin zaɓen fidda gwani na jam'iyyar APC, kuma ga shi an yi rashin sa a ga shi Abdullahi Adamu, Bola Ahmed Tinubu ya zama shugaban ƙasa," in ji Dr Kari.

Ƙarancin dimokraɗiyya a cikin jam'iyyu ya janyo rashin ɗorewar shugabannin manyan jam'iyyu a tarihin siyasar jamhuriya ta huɗu a Najeriya.

Rashin ɗa’a ga Jam’iyya

Kamar yadda ake faɗa a ɓangaren kundin tsarin mulki cewa ' babu wanda ya fi ƙarfin doka' haka ya kamata a ce babu wani ɗan siyasa da ya fi ƙarfin wata jam'iyya.

Kowa ya sani cewa jam'iyya ita ce mafarin siyasar duk ɗan takara, mai neman kansila ko gwamna ko shugaban ƙasa.

A don haka ne a bayan nan jam'iyyu suka riƙa dakatar wa da kuma korar wasu 'ya'aynsu da ke riƙe da muƙamai a mataki na mazaɓu, misali dambarwar da ke tsakanin Sanata Ɗan Juma Goje da jam'iyyarsa da irinta da ta faru tsakanin shugaban jam'iyyar PDP Iyorchia Ayu.

Ko wanne mai mulki a hannu ji yake shi ne ke da iko da jam'iyya.

Su kuma shugabannin da yake ba waɗanda suka cancanta ba ne, naɗa su aka yi dole su yi biyayya da iyayen gidansu da suka kai su kan wannan iko.

Babu shakka an ta ganin yadda 'yan siyasa ke bijirewa umarnin uwar jam'iyya a Najeriya, da kuma yadda jam'iyyun ke karkata zuwa ga tsagen da shugabanni ke so.

Mallakar jam'iyyu d masu iko ke yi

A bayyane ta ke cewa duk gwamna shi ke da ikon jam'iyya a jiharsa, kamar yadda shugaban ƙasa ne ke da cikakken iko da ita a mataki na tarayya.

Wannan ba ya nufin cewa babu shugabannin jam'iyya ko da na riƙo ne, amma tsantsar dabaibaye jam'iyyun da ake yi da badaƙalar siyasa da kuma sanya su a aljihun da ake yi ya sanya shugabannin ke zama tamkar mutum-mutumi.

Irin waɗannan rigingimu na shugabancin cikin gida su ne suka kai jam'iyyar PDP ga faɗuwa zaɓe a babban zaɓen 2015, duk kuwa da cewa su ke riƙe da mulki.

"An ta sauya shugabanni, yau wannan, gobe wannan, suka shiga zaɓen 2015 kawuwansu a rarrabe ƙarshe suka faɗi zaɓe," in ji Farfesa Fagge.

Irin wannan hali dai jam'iyyar APC mai mulki ke ciki a yanzu a Najeriya, sauƙin da nata rikicin zai tarar shi ne babu wani babban zaɓe a gabanta.

Da kuwa a kwai zaɓe a kusa da wataƙila, abin da ya ci doma ba zai bar awai ba, kamar inda masu iya magana ke faɗi.

Dr Kari ya ce matuƙar ana son gyara irin wannan sauye-sauyen shugabannin da ake fama da su, to sai jam'iyyu sun babbatar da dimokraɗiyya a cikin gida.

Su zaɓa wa kansu shugabannin da suke so waɗanda suka dace, wanda a zahiri wannan abu ne mai kamar wuya saboda jam'iyyun an kafa su ne a kan tsarin "kama karya".