You are here: HomeAfricaBBC2023 07 13Article 1803887

BBC Hausa of Thursday, 13 July 2023

Source: BBC

Dele Alli na Everton ya ce an yi lalata da shi yana da shekara shida

Dele Alli Dele Alli

Dan wasan Everton Dele Alli ya ce an yi lalata da shi yana ɗan shekara shida.

A wata hira da ya yi da tsohon ɗan kwallon Ingila Gary Neville, Alli ya bayyana irin cin mutuncin da ya sha tun yana ƙarami kafin a ɗauke shi yana da shekaru 12.

Ya ce an yi masa fyaɗe yana da shekara shida, ya fara shan sigari yana da shekara bakwai kuma ya fara tallar miyagun kwayoyi yana dan shekara takwas.

Alli, mai shekaru 27, kwanan nan ya shafe makonni shida yana jinya saboda jarabar ƙwaya ta barci da kuma matsalolin lafiyar ƙwaƙwalwa.

Ɗaya daga cikin matasa masu hazaka a ƙwallon kafa, Alli ya kasance cikin tawagar Ingila da ta kai wasan kusa da na ƙarshe a gasar cin kofin duniya ta 2018 kuma ya taimaka wa Tottenham zuwa wasan ƙarshe na gasar zakarun Turai a 2019.

Amma bajintarsa ta ragu kuma ya bar Spurs ya koma Everton a watan Fabrairun 2022 kafin ya tafi aro zuwa Besiktas na Turkiyya a bara.

Alli, wanda ya buga wasansa na karshe cikin wasanni 37 na Ingila a shekarar 2019, ya koma Everton a ƙarshen kakar wasan da ta gabata saboda rauni.

Alli ya ce ya fito daga asibiti a Amurka makonni uku da suka wuce kuma inda ya ce abubuwa da dama sun faru da shi a lokacin da yake karami wanda ba zai iya fahimta ba.

A cikin wata sanarwa da Everton ta fitar ta ce: “Kowa a Everton na mutuntawa tare da yaba bajintar Dele wajen yin magana kan matsalolin da ya fuskanta, tare da neman taimakon da ake bukata.