You are here: HomeAfricaBBC2023 07 07Article 1799480

BBC Hausa of Friday, 7 July 2023

Source: BBC

Dokoki huɗu da Shugaba Tinubu ya sanya wa hannu da kuma yadda za su shafe ku

Shugaba Bola Tinubu Shugaba Bola Tinubu

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya sanya hannu a kan umarnin shugaban ƙasa guda huɗu.

Wata sanarwa da fadar shugaban Najeriyar ta fitar a ranar Laraba, ta ce an sanya hannu kan dokokin ne domin rage raɗaɗin haraje-haraje a kan al'ummar ƙasa.

Mafi yawan dokokin na cikin waɗanda gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta ɓullo da su a lokacin mulkinta.

Dokokin dai sun kasu ne zuwa kashi biyu; akwai waɗanda aka tsawaita lokacin da za su fara aiki, sai kuma waɗanda aka dakatar da amfani da su.

Dokokin da abin ya shafa su ne:

1 - Dokar kuɗi ta 2023 (Sauya lokacin da za ta fara aiki): Shugaba Tinubu ya matsa da lokacin da sauye-sauyen da aka yi wa dokar za su fara aiki, daga 23 ga watan Mayu zuwa ɗaya ga watan Satumba, 2023.

Sanarwar da aka fitar ta ce an yi hakan ne domin bayar da wa'adin kwana 90 kafin dokar ta fara aiki kamar yadda dokar haraji ta 2017 ta tanada.

2 - Dokar harajin kwastam (Sauyin lokacin): An sauya lokacin da dokar za ta fara aiki daga 27 ga watan Maris, 2023 zuwa ɗaya ga watan Agusta, 2023.

3 - Dokar harajin kashi 5% na ɓangaren sadarwa (Dakatarwa): Shugaban ƙasar ya dakatar da dokar harajin kashi 5% a kan sadarwa da kuma dakatar da dokar harajin kayan da aka haɗa a cikin gida.

4 - Dokar harajin kare muhalli (Dakatarwa): Dakatar da sabuwar dokar kare muhalli ta a kan amfani da kayan da aka haɗa da roba da kwalabe. Da kuma dakatar da dokar ƙarin haraji a kan wasu motoci da ake shigowa da su ƙasar.

To amma ta yaya dokokin za su taba rayuwar al’ummar Najeriya?

BBC ta tuntuɓi Shu'aibu Idris Mikati, wani masanin tattalin arziƙi a Najeriya domin jin yadda waɗannan dokoki za su yi tasiri ga al'ummar.

Asalin dokokin

Shu'aibu Idris Mikati ya ce a shekarun baya gwamnatin Najeriya ta shiga halin ƙaƙa-ni-ka-yi sanadiyyar rashin isassun kuɗi na gudanar da aiki.

Ya ce "A wancan lokaci kusan kashi 96% na kuɗaɗen da ƙasar ke tarawa ana amfani da su ne wajen biyan bashi."

"A dalilin haka ne gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta ɓullo da wasu daga cikin waɗannan dokokin domin samun ƙarin kuɗin shiga."

Sai dai, ya ce idan aka yi la’akari da abin da ke faruwa bayan kama aikin Bola Ahmed Tinubu a matsayin sabon shugaban ƙasa, an ɗauki wasu matakai masu tsauri, waɗanda ke iya saka talaka cikin matsi.

Daga cikin matakan akwai cire tallafin man fetur da kuma ƙara zubewar darajar naira sanadiyyar ‘barin kasuwa ta yi halinta.’

A dalilin haka ne gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta fara tunanin hanyoyin da za a bi wajen rage raɗaɗin da hakan zai iya haifarwa.

Yadda dokokin za su shafi rayuwar ƴan Najeriya

Mikati ya ce cikin dokokin, akwai guda uku waɗanda za su iya shafar talaka kai tsaye.

Sai dai a cewarsa matakin zai samar da sauƙi ga al’ummar Najeriya ne kawai idan ƴan kasuwa suka samar da rangwame sanadiyyar dakatar da harajin da ake karɓa daga wurin su.

Dokokin su ne na rage ƙarin harajin da ake karɓa kan wasu motoci da ta harajin da ake karɓa daga masu sarrafa kaya a cikin gida sai kuma harajin da ya shafi bangaren sadarwa.

Ya ce “Idan an dakatar da ƙarin da ake karɓa kan kuɗin shigo da nau’ukan motocin da aka ce za a karɓi ƙarin haraji a kansu, ya kamata farashin irin waɗannan motoci ya yi sauƙi, hakan zai haifar da sauƙi a ɓangaren sufuri.”

Haka nan idan aka dakatar da harajin kashi 5% na kayan da ƴan kasuwa ke sarrafawa a cikin gida, to ya kamata su ma farashin kayan da suke sayar wa al’umma ya sauka.

Sai kuma batun dakatar da harajin sadarwa na kashi 5%, wanda ya ce idan masu kamfanonin sadarwa suka yi aiki da ita, za ta yi tasiri kan tsawon lokacin da masu amfani da waya ke ci idan suka sanya katin waya.

Sai dai a cewarsa zai iya yiwuwa ba abu ne da za a gani ɓaro-ɓaro ba.

Inda za a iya samun matsala

Masanin kan tattalin arziƙi ya ce wuri ɗaya da za a iya samun matsala shi ne batun dakatar da sabuwar dokar kare muhalli.

Ya ce "Duniya baki ɗaya na ƙoƙarin yaƙi da sauyin yanayi, kuma ƙasashe da dama sun sanya hannu kan yarjejeniyar rage amfani da makamashi mai haifar da ɗumamar yanayi, kuma Najeriya na daga cikin ƙasashen."

Ya ce "Wajibi ne ga Najeriya ta ɗauki matakan da za su raunana gwiwar al’umma wurin amfani da makamashi mai gurɓata muhalli."

Inda ya ƙara da cewa hukumomi na duniya masu yaƙi da ɗumamar yanayi za su iya ƙalubalantar Najeriya kan hakan, tare da neman Najeriyar ta bayyana hanyoyin da za ta bi wajen rage amfani da irin waɗannan abubuwa masu guraɓata muhalli.

Shin dakatar da dokokin za su rage kuɗin da Najeriya ke samu

Mikati ya ce babu alamun cewa dakatar da dokokin za su zaftare irin kuɗaɗen shiga da Najeriya ke samu kasancewar akwai wasu kafofin samun kuɗin shiga da ƙasar ta buɗe.

Sabbin kafofin samun kuɗin kuwa sun haɗa da abun da za ta samu daga canji kuɗi na ƙasashen waje da kuma ƙarin kuɗaɗe daga tallafin man fetur da aka soke.