You are here: HomeAfricaBBC2023 07 19Article 1808105

BBC Hausa of Wednesday, 19 July 2023

Source: BBC

Evans ya sake komawa Man United

Jonny Evans Jonny Evans

Jonny Evans ya sake komawa Manchester United kan gajeriyar yarjejinyar da zai taka mata leda.

Tuni aka sa sunansa cikin 'yan wasan United da za su buga mata wasannin sada zumunta domin tunkarar kakar 2023/24.

Evans, mai shekara 35, ya fara United tun daga karamar kungiyar, wanda yanzu ke atisaye a Old Trafford, bayan da Leicester City za ta buga Championship a kaka mai zuwa.

Tun farko ana ta hasashen zai koma taka leda a Everton, amma yanzu zai yi wa United wasan sada zumunta da za ta kara da Lyon a Edinburgh ranar Laraba.

Daga nan zai je San Diego tare da karamar kungiyar United, yayin da manyan ke birnin New York.

Evans, ya yi wa tawagar Ireland ta Arewa wasa 102 da buga wa United fafatawa 198 daga nan ya koma West Brom a 2015.

Zaman da Evans ya yi a Old Trafford ya lashe Champions League da Club World Cup da Premier League uku da kuma League Cup biyu.

United ta kuma sanar da cewar Tyrell Malacia da Rhys Bennett na jinya, kenan ba za su buga mata wasa da Lyon ba da wadanda za ta yi a Amurka.