You are here: HomeAfricaBBC2023 05 19Article 1770200

BBC Hausa of Friday, 19 May 2023

Source: BBC

Jami'in da ake zargi da neman cin hanci daga Shah Rukh Khan

Tutar Indiya Tutar Indiya

Shekara ɗaya bayan da aka wanke ɗan shahararren mai fim ɗin Indiya Shah Rukh Khan daga tuhume-tuhumen mallaka da kuma shan ƙwaya, batun ya sake tasowa inda ya mamaye shafukan jaridun Indiya.

Wani jami'i da ke gudanar da bincike kan Aryan Khan - wanda aka kama a Nuwamban 2021 - an tuhume shi da cin hanci da kuma tatsar kuɗi.

Ana zargin Sameer Wankhede da neman cin hancin rupee miliyan 250 kwatankwacin dala miliyan 3.04 daga hannun iyalin jarumin fim ɗin.

A ranar Litinin, yana daga cikin mutum biyar da aka bayyana sunansu cikin wata takardar ƙorafi da aka shigar a sashen binciken manyan laifuka a Indiya.

Hukumar ta ce ana zargin Mista Wankhede da ƙyale mataimakansa su yi wa iyalin Aryan Khan barazana inda ya ce za su yi masa ƙaryar yana ta'amali da ƙwaya idan har bai biya kuɗin ba.

Mista Wankhede ya musanta zarge-zargen inda ya ce "sakamakon da ya samu ke nan a matsayinsa na ɗan ƙasa na gari."

Aryan Khan ko danginsa zuwa yanzu ba su ce komai ba game da batun.

Shari'ar zuwa yanzu...

Mr Wankhede ɗaya ne daga cikin jami'ai uku da suka jagoranci samamen da aka kai cikin Oktoban 2021 kan wani jirgin ruwa inda hukumar da ke yaƙi da miyagun ƙwayoyi NCB ta yi iƙirarin ta ƙwace ƙwayoyi daga Aryan Khan da wasu 19 tare da kama su.

An fitar da Aryan Khan daga cikin jirgin da ya taso daga Mumbai - birnn da iyalinsa ke zama - zuwa Goa.

Hukumar ta NCB ta ce Aryan Khan da sauran mutanen suna tsare ƙarƙashin dokokin da ke da alaƙa da mallaka da sha da kuma sayar da miyagun ƙwayoyi.

Batun dai ya mamaye shafukan jaridu a Indiya da ma duniya. Ɗan jarumin na Bollywood ya shafe kusan mako uku a gidan yari, daga baya kuma an sake shi bayan ba shi beli.

Sai dai a watan Nuwamba ne da aka soki Mista Wankhede kan yadda ya tafiyar da shari'ar aka kuma sauke shi daga muƙaminsa na shugaban hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyi a shiyyar Mumbai.

Nawab Malik, wani ɗan siyasa daga Jam'iyyar Nationalist Congress Party (NCP) wanda ke cikin ƙawancen da ke mulki a Maharashtra a lokacin, ya zargi Mista Wankhede da aikata ba daidai ba lokuta da dama har da tatsar mutane.

Bayan nan ne, shari'ar da ake yi wa Aryan Khan - tare da wasu bincike shida da ba a kai ga yinsu ba - aka ƙace daga hannun Mista Wankhede aka kuma miƙa ta hannun wata tawagar bincike ta musamman.

Wa'adin Mista Wankhede a hukumar ya ƙare a Disamba kuma wata biyar bayan nan, aka mayar da shi sashen karɓar haraji da ke Chennai a Kudancin ƙasar. Rahotanni sun ce ya ci gaba da zama mafi yawan lokuta a Mumbai yana hutu.

Hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyin ta wanke Aryan Khan daga tuhume-tuhumen da ake masa a Mayun 2022.

A watan Agusta, an sake maido da batun bayan da Mista Wankhede ya shigar da ƙorafi gaban ƴan sanda inda ya yi zargin cewa yana fuskantar barazana a kafafen sada zumunta.

A wani ƙorafin da aka shigar a watan, Mista Wankhede ya yi zargi cewa wani babban jami'in hukumar ta NCB yana cin zarafinsa. Jami'in ne yake bincike kan ba daidai ɗin ba da ke tattare da shari'ar ta ƙwayoyi.

Mece ce tuhumar da ake yi wa Wankhede?

Hukumar binciken manyan laifuka CBI ta ce ta soma gudanar da bincike kan Mista Wankhede da wasu mutum huɗu bayan da wani jami'in hukumar NCB ya zarge su da aikata ba daidai ba a ƙarƙashin kulawar Mista Wankhede.

Hukumar ta ce wata tawagar bincike ta musamman daga hukumar NCB ta gano kura-kurai a yadda Mista Wankhede ya gudanar da binciken.

An cire sunayen mutum 17 da ake zargi daga takardun da aka gabatar da ke da alaƙa da shari'ar, in ji hukumar cikin ƙorafinta.

Ta ƙara da cewa Mista Wankhede ya ƙyale farar hula biyu - KP Gosavi da mataimakinsa Sanvile D'Souza - su yi wa tawagar jami'an NCB rakiya a samamen a matsayin shaidu amma sai suka nuna wa waɗanda ake zargi kamar su ne jami'an NCB.

"An bar Gosavi ya je ofishin NCB bayan samamen, abin da ya ci karo da tsarin da ake yi kan shaidu masu zaman kansu," kamar yadda ƙorafin da aka gabatar wa CBI ya nuna. "Ya kuma yi hoton ɗauki da kanka tare da naɗar muryar wanda ake zargi."

A cewar tawagar binciken, hakan ya bai wa Mista Gosavio damar neman rupee miliyan 250 daga iyalin Aryan Khan yayin da ya yi musu barazana cewa zai zargi ɗansu da mallakar ƙwayoyi.

An rage kuɗin zuwa rupee miliyan 180 da kuma Mista Gosavi da Mista D'Souza suka karɓi toshin rupee miliyan biyar a matsayin cin hanci.

Sai dai daga bisani, sun mayar da wani kashi na kuɗin, in ji CBI. Dangin Aryan Khan bai ce komai ba game da zargin.

Ƙorafin CBI ya kuma yi zargin cewa yayin binciken, Mista Wankhede ya gaza samar da gamsassun hujjoji na dukiyarsa kan arzikinsa da ya bayyana.

Me ke faruwa a yanzu?

A ranar Litinin, jami'an CBI sun kai samame kan gidan Mista Wankhede tare da wasu wurare 28 da ke Mumbai bisa alaƙa da shari'ar.

Mista Wankhede ya musanta zarge-zargen da ake yi masa inda ya ce ana "saka masa ne kasancewarsa ɗan ƙasa na gari."

"An sami rupee 23,000 da wasu takardun mallakar dukiya huɗu a gidana," ya faɗa wa manema labarai bayan samamen. "Waɗannan kadarori na same su ne kafin na soma aiki."

A ranar Talata, mai ɗakinsa ta ce zarge-zargen da ake yi masa ba su dace ba.

"Muna bayar da cikakken haɗin kai a binciken na CBI. Mun yarda da doka da oda kuma a shirye muke mu bai wa hukumar da ke bincike haɗin kai a matsayin ɗan ƙasa na gari," Kranti Redkar Wankhede ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na ANI.



Akufo-Addo Reveals List of ... by GhanaWeb Editorial