You are here: HomeAfricaBBC2023 05 19Article 1770212

BBC Hausa of Friday, 19 May 2023

Source: BBC

Ko bashin dala biliyan uku da Ghana za ta ciwo zai fitar da ita daga ƙangin tattalin arziƙi?

Shugaban Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo Shugaban Ghana Nana Addo Dankwa Akufo-Addo

Ghana, da ta kasance babbar kasa a duniya da ke samar da zinare da kuma koko, na fuskantar matsalar tattalin arziki mafi muni da ba ta taba gani ba, inda aka samu hauhawar farashin kayayyaki da kashi 41 a tsawon shekara da ta gabata.

Kasar ta cimma yarjejeniya da Asusun Ba Da Lamuni na Duniya IMF don karbar bashin $3bn na shekara uku domin rage mata matsaloli da take fuskanta.

Ana sa ran cewa za ta karbi kashi na farko na bashin ne na $600m nan ba da jimawa ba, to amma wane sauyi hakan zai yi?

Me ya sa tattalin arzikin kasar ya shiga wani hali?

Ghana, wadda ake kallo cikin sahun kasashen Afirka masu karfin arziki, ta sha shiga tasku musamman ma daga bugun annobar korona da kuma yakin da ake yi a Ukraine.

A watan Oktoban bara, Shugaba Nana Akufo Addo, ya bayyana cewa kasar na cikin matsala ta tattalin arziki.

Sai dai 'yan adawa sun dora laifin matsalar akan almubazzaranci da gwamnati ke yi - zargi kuma da ta musanta.

Hauhawar farashin kayayyaki na ci gaba da karuwa, inda ya kai kashi 41, abu kuma da ya sanya iyalai da yawa ke cikin matsala musamman na samun abinci.

Bashin da ake bin Ghana a yanzu ya kai kashi 90. Gwamnatin kasar ta kasa biyan basukan da ake bin ta, abin da ke nufin sai ta gyara tsarin karbar bashin ta kafin ta samu damar ciyo wanda IMF zai ba ta.

Ana cewa kusan babu komai a cikin baitil-malin kasar a yanzu, abin da jawo mata wahala wajen biyan kudaden shigo da kayayyaki wanda yawanci ake biya da dalar Amurka.

Ganin irin tasku da tattalin arzikin kasar ya shiga ne, ya sa 'yan kasar da dama ke ta daukin jiran wannan taimako daga IMF.

Amma wannan ne karo na 17 tun bayan samun 'yancin kai tsawon shekara 60 da suka gabata, da Ghana ta amince ta karbi bashi daga IMF.

Shin wane sauyi bashin zai kawo?

Duk da cewa Ghana ta kasance babbar kasa da ke samar da koko da kuma zinare a Afirka, daya daga cikin matsaloli da kasar ke fuskanta shi ne ba ta samun isassun kudade a kayayyaki da take fitar wa da kuma zai ba ta damar shigo da wasu kayaki cikin gida.

Wannan dai na cikin abubuwan da ake sa ran rancen na IMF zai taimakawa kasar.

Ana kuma sa ran cewa shirin na IMF zai magance matsalar hauhawar farashi da kuma tabbatar da wadatuwar kudin kasar. Dukkan wannan zai kawo alfanu wa 'yan kasar ta Ghana ta hanyar raguwar farashin kayayyaki, ciki har da wanda ake shigo da shi.

Ana ganin cewa akwai hatsari bai wa Ghana rance, sai dai da sabon shirin na IMF, hakan na nuna cewa kasar za ta iya sake ciyo bashi domin tafiyar da tsare-tsarenta.

Sai dai kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito, kasar za ta sha tattaunawa da masu bayar da bashi, musamman idan ta duba yadda takwararta ta Zambia ta yi.

Kungiyoyin ci gaba, ciki har da Bankin Duniya, sun yi alkawarin taimakawa kasar wajen ganin ta fito cikin matsin tattalin arziki da ta shiga, yayin da ake ganin cewa akwai yiwuwar masu zuba jari su sake dawowa ba tare da wata fargaba ta yin asarar kudadensu ba.

Sai dai, idan aka duba abubuwan da suka faru a baya, ana ganin cewa bashin da IMF zai bai wa kasar ba lallai ne ya magance nakasu da tattalin arzikin kasar ya shiga ba na tsawon lokaci.

Karo na karshe da Ghana ta fice daga shirin na IMF shi ne a 2019, ga shi kuma har ta fara neman kudade da yawa.

Masana sun bayyana cewa dukkan gwamnatoci da suka gabata sun yi almubazzaranci da kudi a tsawon shekaru da suka dauka kan mulki.

Bashin da IMF zai bai wa Ghana na tsawon shekara uku ne, inda mutane ke tambayar ko za a sake shiga mawuyacin hali bayan nan.

Duk da cewa yawancin 'yan Ghana na ganin cewa bashin zai shawo kan matsaloli da ake fuskanta, to amma ba fa ba zai kai ga rage talauci da ya yi katutu ba da samar da aikin yi ko kuma karin kudin albashi, a cewar Godfred Bokpin, Farfesa a fannin tattalin arziki a Jami'ar Ghana.

Ya ce babban kalubale ma na aiwatar da shirin na IMF shi ne shekara mai zuwa, lokacin da kasar za ta gudanar da babban zabe.

Tarihi ya nuna cewa gwamnatoci a Ghana, na da wata al'ada ta kara yawan kudi da ake kashewa gabanin zabukan kasar - domin nuna wa masu zabe irin abin alkhairi da suke yi, ko da kuwa ba su da kudin.

"Gwamnati za ta yi bukatar kashe kudi kuma shirin ba zai ba su damar yin haka ba, zai kai matakin ko su yi watsi da rancen kudin ko kuma su yi wasa da batun zabe," a cewar Farfesa Bokpin.

"Za mu ga yadda bashin na IMF zai hana 'yan siyasa kashe makudan kudade lokacin zabe."

Wadanne sharuda aka gindaya kafin samun bashin na IMF?

Ministan yada labaru na kasar Ghana, Kojo Oppong Nkrumah, ya fada wa BBC cewa gwamnatin kasar za ta kara kudaden shigarta, inda za ta kuma rage wanda take kashewa.

Wannan na nufin cewa za a kara kudaden haraji da ake karba da karuwar farashin ruwa da wutar lantarki da kuma man fetur, a cewar Farfesa Bokpin.

Tuni gwamnatin kasar ta fitar da sabon kudin haraji a kan abubuwa kamar taba-sigari da ruwan lemo da kuma giya da sauransu.

Gwamnatin ta ce ciyo bashin ba shi ne zai fitar da kasar daga matsalolin da take ciki ba.

"Muna da wasu shirye-shirye da za su taimaka mana wajen sake samun ci gaba da tallafawa bangarori masu zaman kansu da kuma magance batun tsadar rayuwa," a cewar Mr Nkrumah.

Ya fada wa BBC cewa gwamnati na da shirin bunkasa masana'antu da aikin gona da kuma samar da karin aikin yi, sai dai jam'iyyar NDC na nuna shakku kan hakan.

Ministan kudin kasar ya ce gwamnati za ta duba yadda za ta rage kashe kudade, sai dai jami'ai sun fada wa BBC cewa ba za a yi wa tsare-tsaren rage talauci katsalanda ba.