You are here: HomeAfricaBBC2024 01 10Article 1910552

BBC Hausa of Wednesday, 10 January 2024

Source: BBC

Liverpool na ƙarancin ƴan wasa daga 11 da take fara kwallo da su

Yan wasan Liverpool Yan wasan Liverpool

Liverpool na fama da ƙarancin ƴan wasa daga 11 da suke fara buga mata wasanni, bayan da take shirin karawa da Fulham ranar Laraba.

Ƙungiyar da Jurgen Klopp ke jan ragama za ta karbi bakuncin Fulham a wasan daf da karshe a Carabao Cup.

Liverpool za ta ci gaba da wasanni ba tare da mai tsaron baya, Trent Alexander-Arnold ba, wanda ya ji rauni a karawa da Arsenal a FA Cup ranar Lahadi.

Mohamed Salah ya je buga wa Masar gasar cin kofin Afirka da za a fara a Ivory Coast daga 13 ga watan nan.

Shi kuwa ɗan kasar Japan, Wataru Endo zai buga wa kasar Asian Cup da za a gudanar a Qatar daga 14 ga watan Janairu.

Ana sa ran Andy Robertson da kuma Kostas Tsimikas za su koma yin atisaye a karshen watan nan.

Har yanzu Dominik Szoboszlai na jinya, yayin da kyaftin, Virgil van Dijk zai fuskanci Fulham ranar Laraba, bayan rashin lafiya da ya yi fama.

Liverpool tana matakin farko a teburin Premier League, sannan ta kai zagaye na biyu a Europa League.