You are here: HomeAfricaBBC2023 06 25Article 1792412

BBC Hausa of Sunday, 25 June 2023

Source: BBC

Man City na son Hakimi, Kungiyoyin Firimiya na rububin Osimhen

Achraf Hakimi Achraf Hakimi

Manchester City na duba yiwuwar saye ɗan wasan Paris St-Germain Achraf Hakimi, mai shekara 24, kuma ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen biyan maƙudan kuɗaɗe a kan sa ba. (Marca - in Spanish)

Manchester United na harin manyan 'yan wasan tsakiya, yayinda da ɗan wasan Brighton & Hove Albion da Ecuador Moises Caicedo, mai shekara 21 ke kan gaba a jerinta, bayan gaza samun cigaba a kokarin farautar Mason Mount. (Sunday Times - subscription required)

United ta nuna rashin jindadinta da Chelsea bayan bankaɗo labarin rashin nasara a cinikin ɗan wasan Ingila Mount, mai shekara 24 ga 'yan jaridu. (Manchester Evening News)

Liverpool da Manchester United da Chelsea za su tattauna da wakilan ɗan wasan Napoli da Najeriya Victor Osimhen, mai shekara 24, a mako mai zuwa kan koma taka leda a Firimiyar Ingila. (Express)

Manyan kungiyoyin Firimiya uku na sa ido kan ɗan wasan Arsenal Eddie Nketiah, mai shekara 24, yayinda kungiyar ke cimma yarjejeniya da ɗan wasan Chelsea mai shekara 24 asalin Jamus, Kai Havertz. (Mirror)

Brighton na zawarcin ɗan wasan gaba a Ajax Mohammed Kudus, mai shekara 22, bayan matashin ɗan wasan asalin Ghana ya yi watsi da tayin Eredivisie. (Mail)

Ɗan wasan tsakiya a Feyenoord da Slovakia David Hancko, mai shekara 25, ya kasance wanda Newcastle United ke zawarci a yanzu. (Mail)

Callum Hudson-Odoi zai tattauna da Chelsea, yayinda kungiyoyin Firimiya da dama ke bibbiyar ɗan wasan mai shekara 22 asalin kasar Ingila. Express)

Everton na son saye ɗan wasan Leeds United asalin Italiya Wilfried Gnonto, mai shekara 19, a wannan kaka. (Football Italia)

Tottenham ta sanya sunan ɗan wasan Wolfsburg Micky van de Ven, mai shekara 22, cikin jeren 'yan wasan da take zawarci, da kuma mai taka leda a Bayer Leverkusen asalin Burkino Faso Edmond Taspoba. (Mail)

Southampton na shirin cimma yarjejeniya da tsohon mai taka leda a Chelsea Derrick Abu, mai shekara 19. (Mail)

Kungiyar Serie A Roma na tattaunawa da mai tsarn baya a Leeds United Rasmus Kristensen. (Mail)

Manchester United na bibbiyar mai tsaron raga a Serbia Djordje Petrovic, mai shekara 23. (Manchester Evening News)

Sheffield United ta shirya sayar da ɗan wasanta asalin Senegal Iliman Ndiaye, mai shekara 23, zuwa Everton a wannan kaka. (Football Insider)