You are here: HomeAfricaBBC2023 08 02Article 1817381

BBC Hausa of Wednesday, 2 August 2023

Source: BBC

Man City ta kulla yarjejeniyar ɗaukar Gvardiol daga RB Leipzig

Josko Gvardiol Josko Gvardiol

Manchester City ta amince da farashin da RB Leipzig ta yi wa mai tsaron bayan Croatia, Josko Gvardiol kan fam miliyan 77.

Cinikin bai kunshi karin tsarabe-tsarabe ba, kenan zai kai fam miliyan 80, irin kudin da Manchester United ta dauki Harry Maguire daga Leicester City.

A shekarar 2019 United ta dauki dan wasan tawagar Ingila a matsayin mai tsaron baya mafi tsada a Birtaniya.

Mai shekara 21 ya zama kashin bayan Leipzig, wanda ya buga mata karawa 87, tun bayan da ya koma Jamus da taka leda daga Dynamo Zagreb a 2021.

Ana sa ran zai je Ingila a cikin makon nan domin a auna koshin lafiyarsa daga nan ya saka hannu kan yarjejeniya.

Watakila kudin cinikin dan kwallon ya kai fam miliyan 86, bayan da tun farko Leipzig ta kayyade, kudin da take son sayar da dan wasan na tawagar Croatia.

Gvardiol, wanda ya ci kwallo biyu a karawa 21 da ya yi wa Croatia, ya taimaka wa kasar ta yi ta uku a gasar Kofin duniya da aka gudanar a Qatar a 2022, sannan ya taimaki Crotia ta yi ta biyu a gasar 'Nations League' a bana, wanda Sifaniya ta lashe.

Sau biyu Leipzig ta buga Champions League tare da Gvardiol, yayin da kungiyar ta yi ta hudu da ta uku a gasar Bundesliga.

Leipzig ta kare a mataki na uku cikin wasannin rukunin champions Leage da City ta yi ta daya a kakar 2021-22.

Sannan ta yi rashin nasara da ci 8-1 a wasa gida da waje da ta buga da City a matakin 'yan 16 a kakar da ta wuce.