You are here: HomeAfricaBBC2023 07 21Article 1809584

BBC Hausa of Friday, 21 July 2023

Source: BBC

Me ya sa masu karɓar haraji a Najeriya ke amfani da zalama?

Wani mai karbar haraji ta Najeriya Wani mai karbar haraji ta Najeriya

Wasu masu kudi a birnin Fatakwal ne dake gabashin Najeriya suka dauki Mista Nwokuha aikin tattara kuɗaɗan haraji, yana riƙe sanda dake tsorata mutane a tituna masu cunkuson ababen hawa.

Aikin mutumin ɗan shekaru 34 shine mai karɓa haraji daga masu tasi da masu manyan motoci da suke aiki a cikin birnin Fatakwal ɗin.

Sana'ar karɓar haraji tsohuwar al'ada ce, a wancan lokacin masu sana'o'i kan bayar da kyautar kudi ko abun sha, domin kyautata alaƙa tsakanin su da manyan gari.

Sai dai yanzu lamarin ya sauya zani, inda masu suka ke bayyana hakan da wani salo na ƙwace.

Wasu daga cikin masu kuɗin na da'awar cewa suna amsar harajin ne a madadin sauran al'umar gari, suna karɓar haraji daga ƴan kasuwa da kuma masu tasi da suke aiki a yankin da suke ganin yana ƙarƙashin ikon su.

Mista Nwokuha ya ce " yana tara naira 5,000-7,000 duk rana, kudi masu kauri a Najeriya.

Yana da mata da yara biyu, kuma bayan ya ɗauki rabon sa yana rabawa wasu masu karfin faɗa a ji su biyar a yankin su, duka kuɗaɗen dai kan zirare tsakanin su.

Gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi a Najeriya kanyi amfani da ire-iren waɗannan mutanen wajen ƙarbar haraji.

"Mutanen na amfani da asusun bankunan su kuma suna cire wani adadi na kuɗin kafin su saka a lalitar gwamnati," a cewar wani tsohon jami'in tattara haraji Michael Ango.

Gwamnatin tarayya a Najeriya ƙarƙashin jagorancin Bola Ahmad Tinubu ta ƙaddamar da hanyoyin tattara haraji na ta na kan ta.

Mista Nwokuha ya yi amannar cewa yana taka muhimmiyar rawa, saboda yana taimakawa wajen sauƙaƙa cunkuson ababen hawa duk da ta haka ne yake saurin damƙe masu tasi.

"Ina sulhunta direbobin tasi idan an samu rikici tsakanin su" inji Mista Nwokuha wanda ke kai gwaro ya kai mari wajen tattara haraji a ranakun litinin zuwa juma'a.

Kafin direba ya tafi zai biya kashi 20 na kuɗin motar fasinjojin da ya ɗauka.

"Ba'a bada dama tasi su dauƙi fasinjoji anan ba." inji Mista Nwokuha yayin da yake nuna wata alama dake gefen titi ɗauke da rubutu kalar na ƴan sanda dake nuni da ba'a tsayawa a wajen.

"Amma idan sun matsa sai sun tsaya a nan to dole su biya kuɗaɗe ga al'umar yankin," kamar yadda ya shaidawa BBC.

A wasu lokuta idan har direba yaƙi biya zasu iya fasa masa madubin gefen direba ko su cire lambar motar shi.

Idan suka yi yunƙurin nuna tirjiya kuwa, sai dai suji bugu a gadon bayan su da sandar dake hannun Mista Nwokuha

Mista Nwokuha yana aikin da ya kamata ma'aikatan ƙananan hukumomi suyi, Najeriya na da yawan ƙananan hukumomi 780 sai dai mafi akasarin su basu aikin su yadda ya kamata.

Kowa zai iya yin irin abunda Mista Nwokuha ke yi madamar zai iya tare motoci a hanya tare da ƙaƙaba matakan da sukayi mashi.

Suna tsayawa a bisa tituna da sanda a hannun su, ko kuma su aje durum-durum a bisa tituna, da karafuna masu tsini saboda direbobin da ke ƙoƙarin tserewa.

Masu karɓar haraji sun fi yawa a kudancin Najeriya, inda suke tsare manyan hanyoyi a madadin wasu gwamnatocin jahohi.

Wani direban babbar mota ya shaidawa BBC cewa yana biyan naira 80,000 kwatankwacin dalar Amurka 100, a duk lokacin da zai je jihar Imo daga Lagos watau tafiyar tsawon kilomita 540.

"A kwai shingen masu tattara haraji guda 15 tsakanin jihar Edo da Fatakwal watau tafiyar kilomita 280," inji direban babbar motar.

Shi ma da yake karin bayani, wani direba ya ce " harajin kashi-kashi ne, akwai harajin da ake kira da na sauraren radiyo da kuma kuɗin ɗaukar fasinjoji da na sauke su."

Ya ce " banda kuɗaɗen da muke badawa na cin hanci ga jami'an tsaro a duk lokacin da muke tafiya a faɗin ƙasar.

Wani jami'a a cibiyar tattara haraji ta Najeriya, Clement Akanibo, ya bayyyana salon na tattara harajin da fashi da makami.

"Yana haifar da wahalhalu wajen yin kasuwanci yana kuma kara kuɗin da mutum zai kashe a kasuwancin sa," inji shi.

Babu wasu bayanai na tsare-tsaren kawo ƙarshen hakan daga gwamnatin Tinubu, amman tabbas yana buƙatar haɗin kan gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi saboda aiki ne da ya shafe su.

Gwamnatin Tinubu ta ce tanason inganta hanyoyin karɓar haraji domin kara kuɗaɗen shiga saboda ta kara adadin kuɗaɗen da za ta kashe a ɓangarorin lafiya da ilimi, tare da rage basususkan da suka dabaibaye ƙasar.

Gwamnatin Tinubu ta yankewa kan ta hukuncin cewa zata bunƙasa kuɗaɗen harajin da take karba shekaru uku masu zuwa.

A yanzu dai gwamnatin Tinubu ta maida hankali wajen karɓar haraji, amma ba ta amfani da masu tare hanya don karɓar haraji, sai dai tana tsammanin ƴan kasuwa su biya kai tsaye zuwa ga asusun gwamnati.

A yunƙurin ta na kawo karshen karkatar da kuɗaɗen haraji, gwamnatin na son ta tabbatar da amfani da hanyar zamani wajen biyan kuɗin, inda ta fara haɗa kai da ƙungiyoyin ƴan kasuwa miliyan 40 masu ƙarfin faɗa a ji.

Hakan ba abu ne mai sauki ba, saboda yawancin ƴan kasuwar ba su aje bayanan kasuwancin su kuma basu taɓa biyan kuɗin haraji ba, ga kuma matsin tattalin arziƙi da ƙasar ke fuskanta.

Sai dai , idan har tsare-tsaren suka yi nasara, gwamnatin Tinubu za ta tilasta gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi daina amfani da hanyoyin al'adar da suka saba amfani ta ita, kuma ƴan Najeriya za su yi murna da hakan saboda za su tsira daga azabtarwar masu ƙwace ire-iren su Mista Nwokuha.