You are here: HomeAfricaBBC2023 05 19Article 1770236

BBC Hausa of Friday, 19 May 2023

Source: BBC

Montana ta zamo jihar Amurka ta farko da za ta haramta wa al'umma amfani da Tiktok

TikTok na daya daga cikin shafukan sada zumunta TikTok na daya daga cikin shafukan sada zumunta

Montana na shirin zama jiha ta farko a Amurka da ta haramta wa al'umma amfani da manhajar nan ta TikTok mallakar ƴan asalin ƙasar China, a wayoyinsu.

Gwamna Greg Gianforte ya sanya hannu kan dokar a ranar laraba. Inda aka tsara cewa dokar za ta fara aiki a ranar ɗaya ga watan Janairu.

Masu manhajar wadda ake amfani da ita wurin yaɗa bidiyo, sun ce haramcin "ya take haƙƙin al'ummar Montana.

TikTok ya fuskanci bincike daga hukumomi daban-daban na duniya game da damuwar cewa za a iya satar da bayanan al'umma tare da miƙa su ga gwamnatin China.

Mista Gianforte, ɗan jam`iyyar Republican, ya fada wa `yan majalisar dokokin cewa haramcin zai ƙara kare mutanen Montana daga masu satar bayanai.

Tiktok ya faɗa a cikin wata sanarwa cewa "dubban ɗaruruwan mutane ne suke amfani da manhajar a jihar ta Montana.

"Muna so mu tabbatar wa al'ummar Montana cewa za su iya ci gaba da amfani da TikTok don bayyana abubuwan da ke ransu, samun abin masarufi, da kuma samun abokai yayin da muke ci gaba da kokarin kare haƙƙin masu amfani da manhajarmu a ciki da wajen Montana."

Ana sa ran TikTok zai ƙalubalanci dokar a kotu.

A watan da ya gabata, `yan majalisa a Montana suka amince da dokar haramta amfani da TikTok a kan wayoyin mutane.

Dokar za ta haramta wa wuraren sauke manhaja sanya TikTok cikin jerin manhajojin da al'ummar jihar za su iya saukewa, sai dai ba za a haramta wa mutanen da ke da ita a wayoyinsu ci gaba da amfani da ita ba.

Montana, wadda ke da yawan jama`a sama da miliyan 1 ta dakatar da manhajar a kan wayoyin ma'aikatan gwamnati a watan Disamban bara.

Tiktok ya ce yana da masu amfani da manhajar a Amurka miliyan 150 ko da yake yawan masu amfani da shi ɗin ya haɓɓaka a cikin yan shekarun nan, har yanzu ita ce manhaja mafi shahara tsakanin yara da matasa.