You are here: HomeAfricaBBC2023 05 19Article 1770242

BBC Hausa of Friday, 19 May 2023

Source: BBC

Na kasa gane abin da ya sa Amurka ta goyi bayan zaɓen Tinubu - Atiku

Atiku Abubakar Atiku Abubakar

Ɗan takarar babbar jam'iyyar adawar Najeriya, Atiku Abubakar ya nuna takaici a kan goyon bayan da Amurka ta bai wa zaɓaɓɓen shugaban ƙasar, Bola Ahmed Tinubu.

Ya ce karya gwiwar 'yan Najeriya ne, Amurka ta halatta zaɓen da "ɓangarori da yawa suka ɗauka a matsayin zaɓen almundahana a Najeriya".

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, kuma ya ja hankalin Sakataren wajen Amurka Anthony Blinken da Ma'aikatar harkokin wajenta, Atiku Abubakar ya bayyana matuƙar mamaki kan yadda Anthony Blinken ya kira zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Bola Tinubu ta wayar tarho.

Da safiyar Larabar nan ne, Sakatare Blinken ya kira Bola Tinubu ta wayar tarho inda ya bayyana ƙudurin Amurka na aiki tare da gwamnatin zaɓaɓɓen shugaban Najeriyar, ta hanyar ƙarfafa hulɗar dangantaka.

Yayin tattaunawar, Blinken ya ce ƙasashen biyu sun ɗauki tsawon lokaci suna da kyakkyawar hulɗa, don haka zai so ganin ɗorewar hakan a ƙarƙashin mulkin zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Tinubu.

Tinubu da Blinken sun kuma tattauna kan muhimmancin kafa gwamnatin da za tafi da duk ƴan Najeriya da ƙara inganta tsaro da kuma kawo tsare-tsaren da za su taimaka wajen ci gaban tattalin arzikin ƙasar.