You are here: HomeAfricaBBC2023 08 02Article 1817363

BBC Hausa of Wednesday, 2 August 2023

Source: BBC

Ousmane Dembele zai koma PSG in ji Xavi

Ousmane Dembele Ousmane Dembele

Ɗan ƙwallon Barcelona, Ousmane Dembele zai koma taka leda a Paris St-Germain, kamar yadda koci Xavi ya tabbatar.

Mai shekara 26, ɗan kwallon tawagar Faransa ya yi zaman benci a karawar da Barcelona ta ci AC Milan 1-0 yayin wasan sada zumunta da suka kara a Las Vegas ranar Laraba.

''Ya sanar da ni cewar an tuntuɓe shi, kuma ya yanke shawarar barin Barcelona, wannan zaɓinsa ne, ''in ji Xavi.

Dembele ya ci kwallo 40 a fafatawa 185, tun bayan komawarsa Barcelona daga Borussia Dortmund a kan fam miliyan 135 cikin 2017.

A bara ne, Dembele ya sa hannu kan yarjejeniyar tsawaita zama a ƙungiyar, bayan kammala kakar da ya taka rawar gani a ƙungiyar ta La Liga.

Yana cikin 'yan wasan tawagar Faransa da suka kai ta gurbin shiga kofin duniya a Disamban 2022 a Qatar, amma jinya ba ta ba shi damar zuwa gasar ba.

Ranar Asabar Dembele ya ci ƙwallo a karawar da Barcelona ta ci Real Madrid 3-0 a wasan atisayen tunkarar kakar bana da suka yi a Amurka.

PSG ta lashe Ligue 1 guda tara a cikin kaka 11.

Ranar Asabar Dembele ya ci ƙwallo a karawar da Barcelona ta ci Real Madrid 3-0 a wasan atisayen tunkarar kakar bana da suka yi a Amurka.

PSG ta lashe Ligue 1 guda tara a cikin kaka 11.