You are here: HomeAfricaBBC2023 05 19Article 1770218

BBC Hausa of Friday, 19 May 2023

Source: BBC

Ramsdale ya saka hannu kan ci gaba da kama gola a Arsenal

Aaron Ramsdale Aaron Ramsdale

Aaron Ramsdale ya saka hannun kan doguwar yarjejeniyar ci gaba da tsare raga Arsenal.

Sai dai Gunners ba ta fayyace tsawon kakar da golan zai yi a Emirates ba, amma Mikel Arteta ya ce ya yi farin ciki da zai ci gaba da aiki da Aaron.

Ramsdale, mai shekara 25, ya buga wasa 36 a Premier League da Gunners, wadda ta kalubalanci lashe kofin bana.

Ramsdale, wanda tun farko kwantiraginsa zai kare a karshen kakar 2025 ya koma Gunners daga Sheffield United a Agustan 2021, kan yarjejeniyar fam miliyan 24 da karin fam miliyan shida kudin tsarabe-tsarabe.

Wanda ya buga wa tawagar Ingila wasa uku, ya kama gola wasa 13 kwallo bai shiga ragarsa ba a kakar nan.

Arsenal tana mataki na biyu a teburin Premier League da tazarar maki hudu tsakaninta da Manchester City, wadda ke jan ragama mai kwantan wasa.

Idan Arsenal ta kasa cin Nottingham Forest ranar Asabar, kofin Premier ya zama na City na biyar a kaka shida.

Haka kuma City za ta iya daukar kofin bana da zarar ta yi nasara a wasa daya daga ukun da yake gabanta, wadda za ta kece raini da Chelsea ranar Lahadi.

Sauran wasannin da za ta buga shine da Brighton da kuma Brentford.