You are here: HomeAfricaBBC2023 08 02Article 1817360

BBC Hausa of Wednesday, 2 August 2023

Source: BBC

Wata alkaliya a Sifaniya ta tuhumi Dani Alves da laifi

Dani Alves Dani Alves

Wata alƙaliya a Sifaniya ta tuhumi tsohon dan wasan Barcelona da tawagar Brazil, Dani Alves, wanda yake tsare kan zargin fyade a watan Janairu.

An tsare Alves ne bisa zargin cewar ya ci zarafin wata mace a Barcelona a wani gidan rawa cikin watan Disamba.

Mai shari'ar ta ce ta samu wata shaidar da ta fayyace cewa ɗan ƙwallon mai shekara 40 ya aikata laifin.

An ɗaure Alaves a kurkuku, ba tare da bayar da shi beli ba.

Lauyan dan kwallon ya ce, Alves ba zai haƙura ba wajen ɗaukaka ƙara ko da an same shi da laifi a kotu.

A Sifaniya, idan an samu mutum da laifin fyade, za a iya ɗaure shi tsawon shekara 15 a gidan yari.

Mai shigar da ƙara zai miƙa wa kotu tuhuma, daga nan a tsayar da ranar da za a fara sauraron ƙarar.

Alves ya buga wa Barcelona wasa 408 da lashe La Liga shida da Champions League uku, yana cikin tawagar Brazil da ta lashe kofin duniya a 2022.

Ƙungiyar da ya buga wa tamaula kwanan nan ita ce Pumas UNAM, wadda a watan Janairu ta soke sauran ƙunshin yarjejeniyar da take tsakaninsu.