BBC Hausa of Friday, 12 January 2024

Source: BBC

'Ya kamata Tinubu ya dakatar da Matawalle kan rashawa'

A Najeriya y ayin da ake zaman zullumi da jiran hukuncin kotun koli, wata sabuwar cacar baka ce ta barke tsakanin gwamnatin Dauda Lawan Dare ta PDP a jihar Zamfara da tsohon gwamnan jihar kuma karaminin ministan tsaro Dr Bello Matawalle.

Gwamnatin Dauda ta ce dakatar da ministar jinkai da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi ya nuna ana iya dakatar da karamin ministan tsaro da ta dade tana zargi da wawushe dukiyar Zamfara.

Sai dai tsohon gwamnan ya musanta, tare da cewa hassada ce kawai saboda ya zama minista.

Gwamnatin Dauda Lawal ta ce tun da aka dauki matakin dakatar da Betta Edu, to bai kamata shi ma Matawalle ya sha ba kamar yadda Mustrapha Jafaru Kaura babban matakimaki ga gwamnan jihar Zamfarar Dauda Lawan Dare ya shaidawa BBC.

Ya kara da cewa: ''Tun da EFCC shawara aka ba ta da ta kai ga daukar mataki a kan ministar ma'aikatar jin kai, me ya sa ba za ta dauki mataki kan Bello Matawalle ba? wanda an yi bincike akan shi kuma tsohon shugaban hukumar EFCC Abdurrashid Bawa ya fada rigar kariya da kundin tsarin mulki ya bai wa gwamnan ce ta hana su daukar mataki. Amma maimakon mu ga an yi wani abu bayan ya sauka daga mukamin sai kawai muka gan shi a matsayin Ministan tsaro.''

Wannan dai tsohuwar dambarwa ce aka sabunta tsakanin gwamnatin Dauda Lawan dare ta PDP da kuma wanda ya gada Bello Matawalle na APC kuma karamin ministan tsaro wadanda dukkanin ke jiran sanin makomarsu a kotun koli.

Sai dai bangaren Matawalle ya yi watsi da zarge-zargen, kuma Rabi'u Garba tsohon kwamishinnan kudi na jihar, sannan na hannun damar tsohon gwamnan Zamfara kuma karaminn ministan tsaron Najeriya ya ce bakin ciki kawai ake musu.

''Ita wannan magana ta Bilkiyan 70 an yi ne domin a bata masa suna saboda kada ya zama ministan tsaro, kuma ba a taba nada ministan tsaro da ya yi nasara cikin kankanin lokaci kamar Bello Matawalle ba.

Kudin da ake maganar an ci bashi a cikin shekaru hudu aka yi amfani da su, a bincika nawa muka biya kudin albashi, da fansho da sauransu? Dan haka mu duk maganganun da suke yi ba su dada mu a kasa ba,'' inji Rabi'u Garba.

Tun hawanta mulki, gwamnatin PDP a Zamfara ke takun-saka da tsohuwar gwamnatin Apc ta Matawalle da ta ke zargin rashawa da wawushe kuɗaɗen jihar.

Kuma rikicin siyasar jihar zai iya kara daukar hankali da tsamin adawa tsakanin bangarorin biyu musamman bayan hukuncin kotun koli da zai tabbatar da bangaren da zai ci gaba da jan ragamar tafi da gwamnatin jihar.