You are here: HomeAfricaBBC2023 06 25Article 1792409

BBC Hausa of Sunday, 25 June 2023

Source: BBC

Yadda girman halittar 'mamana' ke hana ni sakewa

Jackie Adedeji Jackie Adedeji

Kunya da zafi - kalmomi biyu ke nan da mata suke amfani da su wajen bayyana irin halin da suka shiga saboda girman 'mama'.

Jackie Adedeji na ganin samun manya-manyan 'mama' abu ne da ba a ɗauka da muhimmanci inda ta ce muna kallon su ne a matsayin 'abin dariya' a Birtaniya.

Ta ce kasancewar girman mamanta ya kai 36K na nufin akwai lokutan da a rayuwarta take son ɓoye kanta.

"Tun daga shekara kimanin 11 ake nuna ta, na tuna lokacin da nake tafiya makaranta sai manyan maza su riƙa wuce ni suna lasar laɓɓansu," kamar yadda ta shaida wa BBC Newsbeat.

"Na kuma kasance cikin taruka inda abokan aikina suke ƙura min ido, suna sa na ji wani iri."

Jackie, wadda ta yi bayani kan waɗannan batutuwa a wani shiri na Channel 4 da aka yi wa taken My Big Boobs: Abin da ba a sani ba, ta ce ta koyi ta rungumi yanayin jikinta.

Sai dai akwai mata da yawa da ake yi wa tiyata kuma abu ne da yake neman zama ruwan dare.

Ƙungiyar likitocin gyaran jiki BAAPS ta ce rage girman 'mama' shi ne abu na biyu mafi fice a aikin fiɗar jiki.

Ta ce akwai mata 5,270 da suka rage 'mamansu' a 2022, kusan kashi 120 daga bara sannan sama da haka gabanin lokacin korona.

Jackie ta ce ba ta tunanin mutane sun san "halin da mata suke ciki" idan suna da ƙatoton 'mama'.

"Suna jin kunya saboda mutane da yawa suna ganin sun mallaki 'mamanki' idan suka kasance manya, ana kallon su a matsayin mallakin jama'a," in ji ta.

Kuma tana fama da matsin lamba ta al'ada - ta tashi a gidan da ke riƙo da addini inda ake tsammanin ta kasance cikin shiga ta mutunci.

"Ya kamata ka zama mai ado kuma a matsayina ta mace baƙar fata, kana son kullum ka nuna kanka a yanayi mai kyau kuma ina yawan ji cewa ba a kallon 'mamana' a matsayin abu mai kyau."

'A ƙyale ta'

Amber ma ta kasance cikin irin wannan yanayi - ta kuma yanke shawarar keɓe kanta a farkon 2022.

Bayan shekarun da ta shafe cikin yanayin damuwa da fuskantar zafi saboda girman mamanta da ya kai 36I, aikin tiyatar an tsammace shi ga matashiyar mai shekara 26 daga Cornwall.

"Tun bayan da na gama makaranta, na kasance cikin fama, amma bayan na shayar da ƴata sai zafin ya kai ma ba na iya tafiya lafiya," in ji ta.

Da farko, ta yi ƙoƙarin yin tiyata ƙarƙashin NHS amma sai suka ki amincewa da hakan lokuta da dama.

"Ni da mijina mun tattauna sosai kuma mun yanke shawarar karɓar bashi," in ji Amber, wadda ta nemi mu ɓoye sunan mahaifinta.

"Duk da cewa akwai matsalar rashin kuɗi, yin tiyatar shi ne mataki mafi kyau da na ɗauka."

Rage girman 'mama' ba wani abu ne na musamman na samun dama a NHS ba kuma kamar sauran aikin fiɗa, ana samun dogayen layuka.

Wata da ta yi ƙokarin samun tiyata a NHS ira ce Racheal mai shekara 28.

Amma hakan ya faru shekara 10 bayan ta tuntuɓi likitanta kan fama da ciwon baya da damuwa saboda yadda ake tsokanarta kan girman 'mamanta' da ya kai 34HH.

An nemi Rachael ta rage nauyinta duk da nauyin jikinta bai wuce ƙa'ida ba, kuma sai da aka gano tana fama da ciwon baya mai tsanani ne ta ji kamar an ɗauke ta da muhimmanci.

"Na yi ƙoƙarin shan maganin disashe raɗaɗi da yin atisaye na tsawon wata shida kafin a saka ni cikin jerin waɗanda ke dakon tiyata kuma sai da aka ɗauki shekara biyu tun daga nan," in ji ta.

Rachael - wadda ba za mu yi amfani da sunan mahaifinta ba - ta saka kanta cikin masu matuƙar sa'a inda ta ce rayuwarta bayan tiyatar ta fi ta baya.

"Kafin tiyatar, bana iya gudu ba tare da na kasance cikin raɗaɗin zafi ba. Wannan ita ce ɗaya daga cikin babbar nasara.

"A yanzu na fi jin daɗin jikina fiye da baya."

Me ya sa mata suke rage girman 'mamansu'?

Mataimakiyar shugaban ƙungiyar BAAPS Nora Nugent ta ce mata na yin haka ne saboda aikin ya fi tasiri, yana kuma ƙara kyau.

"Yana taimakawa wajen gyara jiki da kyawun sura ko abubuwa kamar kaya su yi wa mutum das," in ji ta.

Likitar fiɗar ta kuma ce a yanzu ba a ƙyamatar tsarin.

"Tsawon lokaci, akwai wani sirri game da fiɗa kuma duk da cewa rage girman mama ba wai kwalliya ba ce, ya faɗa ƙarƙashin wannan rukuni.

"Don haka mutane ba su cika magana a kai ba. A yanzu, abin a bayyane yake."

Hanyar da ake bi don samun tiyata

NHS England ta faɗa mana cewa mutane sun amince da yanayin jikinsu bayan tiyatar rage 'mama' - kuma hakan ya haɗa da yadda suke tantance wanda za a iya yi wa tiyatar da wanda ba za a iya yi wa ba.

Tsarin yana farawa ne daga ganin likita inda za a tantance marasa lafiya a gano matsaloli kamar ciwon baya da na wuya da matsalolin damuwa.

Idan likita ya ga mutum ya dace a yi masa tiyata, za a baka likitan 'mama' amma za ka iya kasancewa cikin jira kafin a tantance ka.

Wata tawaga ce take yanke shawara ta ƙarshe.

Ga Jackie, ta san labarinta ba zai rage yawan mutanen da ke jira ba amma fatanta shi ne zai sa mutane su kasance masu tausayi.

"Zan zo na ga ana yawan tausaya wa mata masu girman 'mama' saboda ina son mutane su gane cewa idan suka ga mace tana wucewa kan titi kuma ta kasance mai girman 'mama' tana fuskantar abin da ke gabanta, a ƙyale ta."