You are here: HomeAfricaBBC2023 04 17Article 1750829

BBC Hausa of Monday, 17 April 2023

Source: BBC

Wane hali ɗaliban Najeriya ke ciki a Sudan?

Hoton alama Hoton alama

Yayin da ake ci gaba da gwabza fada tsakanin sojojin gwamnatin Sudan da sojojin da ba na gwamnati ba, a lamarin da ya bayyana karara yunkurin juyin mulki ne, dalibai 'yan Najeriya da ke karatu a jami'oi'i daban-daban a kasar sun bayyana wa BBC halin da suka samu kansu a ciki a wannan lokaci.

Muhammad Nura Bello, shugaban kungiyar dalibai na jami'ar Sudan International University a birnin Khartom, ya ce sun samu kan su cikin wani hali na zaman dar dar, inda ya ce tun daga ranar Asabar da safe da ya farka da jin karar harbe-harbe babu kakkautawa.

Ya kuma kara da cewa lokacin ne ya duba wayarsa ya rika ganin sakonni da kiraye-kirayen waya cewa akwai fadan da ya barke a cikin gari da kuma zagayensu, kasancewa akwai wasu sansanonin soji a kusa da su.

Shugaban daliban ya bayyana cewa da yake suna magana da ‘yanuwansu dalibai, saboda a matsayin wakilinsu ya zama dole ya rika tunanin ya yanayin su yake a halin da ake ciki, kuma suna bai wa junansu bayanai da shawarwari kan abubuwan da suka kamata su yi, da kuma yanayin da ake ciki.

‘’Da yake akwai yanayi na fargabar mutum bai saba ganin kan shi cikin yanayi na tashin hankali irin wannan ba, muna magana da juna, muna da group wanda muke tuntubar juna bayan sa’oi ashirin da hudu ko kafin nan ma, muna kokarin tattaunawa da junanmu kan halin da ake ciki, ya ce.’’

Muhammad Nura ya kuma ce babu wani daga cikin dalibai ‘yan Najeriya da suka samu labari wani abu ya same su, sun kuma yi kokarin ganin shugabannin makarantun da yawa sun tura wa dalibai wasikun cewa kowa ya zauna a gida.

Ya kuma kara da cewa: ‘’Muna tuntubar juna da ofishin huldar jakadancin Najeriya a nan, sun ce mu kwantar da hankulanmu idan akwai wani abu, za su neme mu, idan kuma akwai wani abu sai mu tuntube su.’’

‘’A matsayinmu na dalibai fatanmu shi ne Allah ya kawo daidatuwa a samu a sasanta don dalibai su ci gaba da karatunmu.’’

Wata daliba a Omdurman

Ita ma wata dalibar Najeriyar da ke zaune a birnin Omdurman mafi girma a kasar ta Sudan da ke gabar yammacin kogin Nilu a arewa maso yammacin birnin Khartoum, ta shaida wa BBC cewa sun shiga cikin wani hali na rashin tabbas da fargaba.

Ta kuma ce suna zaune a cikin gida ba su san me yake faruwa a waje ba, Gaskiya ba zan iya cewa ga halin da muke ciki ba, ko tagagogin gidajensu ba sa budewa saboda fargaba, amma kuma babu abin da suke ji sai karar harbe-harbe da tashin bama-bamai.

‘’Mu kan ji karar wucewar motoci jefi-jefi, ko kuma jiragen yaki na ta shawagi a sama, da karar tashin abubuwan fashewa da na bindigogi su muke ta ji a koda yaushe muna daga cikin gida, in ji ta.’’

Kamar dai sauran wasu birane a cewar dalibar, an samu daukewar wutar lantarki a yankuna da dama, kana an dauke ruwan famfo har yanzu kuma babu alamar ko kadan.

‘’Babbar matsalar ma ita ce ba ma samun mu yi cajin wayoyinmu saboda yawan katsewar wutar lantarkin, wadda muke da tsananin bukata don mu rika sanin halin da ake ciki a waje tun da muna cikin gida a kulle, a cewar dalibar.’’

An gargade mu da mu rika kwantawa a kasa

Dalibar ta kuma bayyana cewa kungiyon daliban Najeriya a kasar na ba da shawarwari tare da gargadi kan matakan tsaron da ya kamata su rika dauka saboda yiwuwar tashin bama-bamai sakamakon wannan artabu da ake yi.

‘’Wadanda muke tare da su yawanci sun kwanta a kasa, ni dai na kwanta a kan katifa amma na sauka daga kan gado, saboda wannan gargadi, ta ce.’’

Sai dai kuma in ji ta a unguwar da suke in baya da jin karar tashin bama-bamai da harbe harben, ta kan ji a wasu lokuta mutane kan fito suna harkokinsu a cikin layukan unguwannin nasu.

Muna son mu koma gida Najeriya

Muhammad Nura Bello shugaban daliban Najeriya ya bayyana cewa a halin da suka tsinci kan su yanzu haka babu abin da suke bukata sai su ga cewa sun koma gida Najeriya saboda zaman rashin tabbas na tashin hankalin da ke faruwa tsakanin sojojin gwamnati da wadanda ba na gwamnati ba.

‘’A halin yanzu dalibai da yawa hankalinsu ba a kwance yake ba, har da su kan su iyayen dalibai suna ta kiran mu cewa a yi kokari a yi magana da jami’an diplomasiyya na Najeriya su yi kokari kowa ya koma gida Najeriya, in ji shi’’

‘’Mu kanmu muna son mu koma gida kasancewar yanzu wuri ne wanda ba kasarku ba baka da tabbaci kan yadda yanayin tsaron lafiyarka yake, kasancewa a koda yaushe kana ta jin karar harbe -harben bindigogi da makamantansu.’’

Ya kuma kara da cewa ‘’Akwai matsalar abinci da ruwan sha, da wutar lantarki ba ka san yadda abubuwa za su kara kasancewa ba, dole muna bukatar gwamnati da duk wasu masu ruwa da tsaki da su taimaka don mu samu mu koma gida, in ya so idan komai ya daidaita sai mu komo mu ci gaba da karatu.’’

Tashin hankalin dai ya kara ta'azzara ne sakamakon gwagwarmayar neman iko tsakanin babban hafsan rundunar soji kuma jagoran Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan da mataimakinsa da ke iko da dakarun RSF, Janar Hamdan Dagalo wanda aka fi sani da Hemeti.

Tun bayan karkatar da wani juyin-juya-halin fararen hula da ya hamɓarar da Shugaba Omar al-Bashir wanda ya daɗe a kan mulki a 2019, rundunar sojin ta tattare iko a hannun jami'anta.