BBC Hausa of Saturday, 6 January 2024

Source: BBC

Mata sun ƙona fadar hakimi a jihar Filato

Hoton alama Hoton alama

Waɗansu mata da suka yi da zanga-zanga a garin Bokkos da ke jihar Filaton Najeriya sun banka wa fadar hakimin garin na Bokkos wuta, sakamakon harzuka da suka yi game da kame-kamen mutane da jami'an tsaro ke yi a yankin, bayan wasu hare-hare da suka auku a kwanakin baya.

Sai dai bayanan da aka samu sun ce wani ɓangare ne na fadar aka ƙona, kuma ba a yi asarar rai ba sakamakon wutar.

Matan na zargin cewa jami'an soja sun shiga yankin suna tattara matasa ba tare da wani dalili ba.

Wata shugabar matan yankin da lamarin ya auku a idonta, Laraba Lekshak, ta ce matan da suka tayar da hankalin sun tunkari fadar ne yayin da wasu shugabannin matan yankin ke ziyartar hakimin domin tattaunawa kan hare-haren da suka auku a ranar jajiberin Kirsimeti.

'Mun shiga kenan za mu zauna sai muka ji ana ruwan duwatsu, ana fasa windoji, da muka fita muka haɗu da matan sai muka fara ba su hakuri, amma ba su saurare mu ba. Ana cikin haka sai suka fito da fetur suka ƙona fadar, suka ƙona motoci, mu ma da ƙyar muka fita daga wurin,' in ji ta.

Ta ƙara da cewa shugabannin matan yankin sun yi Allah-wadai da abin da matan suka aikata kuma ba su goyin bayan matakin da matan suka ɗauka ba.

A cewarta 'idan abu ya lalace ba da faɗa ake magance shi ba ya kamata a zauna ne a teburin sasantawa.'

Shugabar matan ta yi kira da a nemi hanyyoyin da za a iya warware duk wata matsala cikin kwanciyar hankali ba tare da an tayar da jijiyar wuya ba.

Wani mai riƙe da mukami a garin na Bokkos, Chief Gabriel Loms ya ce ɓangaren ofisoshin fadar ne wutar ta shafa kuma ba a sami asarar rai ba. Ya kuma bayyana cewa sun ɗauki wannan lamari da matuƙar muhimmanci.

'Mu yanzu muna ba su hakuri ne, mu waɗanda ke riƙe da sarauta za mu zauna da sarki, mu kira matan domin mu tattauna, saboda mu ji shawarwarinsu na nemo hanyoyin da za a warware matsalolin.'

Ya ce akwai buƙatar mutanen yankin su ƙara hakuri saboda gwamnati ta fara ɗaukar matakai bayan hare-haren da aka kai kuma za a yi nazari domin tabbatar da hakan bai sake faruwa ba.

BBC ta yi yunƙurin ji ta bakin jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar amma bai amsa kiran da aka yi masa ta waya ba.

Bayanai da aka samu sun nuna cewa an ƙara yawan jami'an tsaro da ke fadar hakimin na Bokkos da kuma sauran sassan yankin domin tabbatar da zaman lafiya.