BBC Hausa of Wednesday, 10 January 2024

Source: BBC

Yadda ƴar TB Joshua ta tona asirin abubuwan da mahaifinta ya aikata

Ajoke ta sawke sunan ubansa 'Joshua' Ajoke ta sawke sunan ubansa 'Joshua'

BBC ta gano yadda mamallakin katafaren cocin nan na Najeriya Synagoge, TB Joshua, wanda aka zarga da aikata fyade kan mabiyansa, ya garkame ƴarsa a ɗaki, ya azabtar da ita na tsawon shekaru kafin daga baya ya yi watsi da ita tana gararamba a birnin Legas da ke Najeriya.

Gargaɗi: Wannan labari na ɗauke da abubuwa masu tayar da hankali.

"Mahaifina yana da tsoro, yana da matukar tsoro. Yana fargabar cewa akwai wanda zai fita ya yi magana," a cewar ɗaya daga cikin ƴaƴan limaman cocin, Ajoke - wadda ta fara fitowa ta faɗa wa BBC irin cin zarafin da ta fuskanta a cocin mahaifinta, the Synagogue Church of All Nations (Scoan).

TB Joshua, wanda ya rasu a 2021 yana da shekara 57, an zarge shi da cin zarafi da kuma gallazawa a majami'arsa na tsawon shekara 20.

Ajoke, wadda ke da shekara 27 da haihuwa a yanzu, tana rayuwa ne a ɓoye kuma ta soke sunan mahaifinta na da "Joshua" - BBC ba za ta wallafa sabon sunanta ba.

Babu wani takaimaimen abu da aka sani kan mahaifiyar Ajoke, wadda aka yi imanin cewa tana ɗaya daga cikin mamba a cocin Joshua. Ajoke ta ce ta girma a hannun matar TB Joshua mai suna Evelyn, tun daga yarunta.

Ajoke ta ce ta yi rayuwar farin ciki har zuwa shekara bakwai, inda suka riƙa tafiya hutu tare da iyalan Joshua zuwa wurare irin su Dubai.

Sai dai kwatsam, abubuwa suka sauya a wata rana. An dakatar da ita daga makaranta saboda wani ɗan ƙaramin laifi da ta yi, kuma wani ɗan jarida ya rubuta wani labari inda ya kwatanta ta da ƴar TB Joshua da aka haifa ba tare da aure ba.

An cire ta daga makaranta tare da tafiya da ita zuwa harabar cocin ta Synagogue da ke Legas.

"An kai ni zuwa ɗakunan mukarraban Joshua. Ban nuna sha'awar zama cikin mukarrabansa ba. An buƙaci na shiga," in ji Ajoke.

Mukarraban sun kunshi mabiya masu hazaka waɗanda suka yi wa TB Joshua aiki tare kuma da yin rayuwa da shi a cikin cocin mai cike da abubuwa masu sarƙaƙiya.

Sun fito ne daga sassa daban-daban na faɗin duniya, inda wasu ke zaune a cocin na tsawon gomman shekaru.

Sun yi rayuwa ne ƙarƙashin tsauraran dokoki: An haramta musu yin barci na sa'o'i da yawa a lokaci guda, an haramta musu yin amfani da wayoyinsu ko kuma duba sakonninsu na imel, da kuma tursasa musu kiran TB Joshua a matsayin "Uba".

"An tursasa wa muƙarraban yin abubuwa da dama. Kowa na aiki ne bisa umarni. Babu wanda ke tambayar komai," in ji ta.

A matsayinta ta yarinya, Ajoke ba ta bi dokokin da aka saka a cocin ba kamar sauran mukarrabai: Ta ƙi miƙewa tsaye a lokacin da faston ya shiga ɗakin, kuma ta ƙalubalanci irin yanayin kwanciya da suke yi.

Jim kaɗan, sai aka fara cin zarafin su.

Ba ta jima da isa ba, lokacin da take ƴar shekara bakwai, ta tuno yadda aka lakaɗa mata duka saboda fitsarin kwance inda aka kuma tursasa ta zagaya harabar cocin sanye da wata alama a wuyanta da ke cewa "Ni mai fitsarin kwance ce."

"An ce Ajoke na da baƙaƙen aljanu wanda take buƙatar a cire mata," in ji wata tsohuwar ta kusa da Joshua a cocin.

"Akwai wani lokaci a wajen taron muƙarrabai - shi (Joshua) ya ce mutane za su iya duka na. Ko waye a cikin ɗakunan mata duka na kawai suke yi kuma nakan tuna lokacin da mutane ke sharara min mari idan suka zo wucewa," in ji ta.

Daga lokacin da Ajoke ta koma cocin a Ikotun da ke jihar Legas, ta shiga mawuyacin hali na gallazawa.

"An ɗauki karan-tsana an saka mata a cikin iyalan," in ji Rae daga Birtaniya, wadda ta shafe shekara 12 tana rayuwa a cocin cikin mukarrabai. Kamar sauran tsoffin muƙarraban cocin da BBC ta tattauna da su, ta zaɓi yin amfani da sunanta na farko kaɗai.

Rae ta tuno wani lokaci da Ajoke ta yi barci na tsawon lokaci, inda Joshua ya daka mata ihu da cewa ta tashi.

Wata cikin mukarraban cocin ta ɗauke zuwa wurin yin wanka, inda ta ɗauki wayar wutar lantarki ta rika dukanta tare kuma da fesa mata ruwa mai zafi," in ji Rae.

Da take tuno al'amarin, Ajoke ta ce: "Na yi ta yin ihu, kuma sun bar ruwan zafin ya yi ta zuba a kaina har na tsawon lokaci."

Irin wannan cin zarafin ya ki karewa, in ji ta.

"Muna magana ne a kan cin zarafi na tsawon shekaru. Cin zarafi a kodayaushe. Kasancewa ta a matsayin ƴarsa da aka haifa ba tare da aure ba ya ƙara dagula komai da shi (TB Joshua) ya ce yana faɗa a kai."

Cin zarafin ya yaɗu zuwa mataki daban-daban lokacin da take shekara 17 kuma ta fuskanci mahaifinta kan "mutanen da suka gamu da cin zarafi na lalata".

"Na ga wasu mukarrabai mata na shiga ɗakinsa. Suna ɗaukar tsawon sa'o'i a ciki. Ina jin abubuwa: 'Kash wannan abin ya faru da ni. Yayi ƙoƙarin kwanciya da ni. 'Mutane da yawa na faɗan abu iri ɗaya," in ji ta.

BBC ta tattauna da mata mukarrabai sama da 25 - daga Birtaniya, Najeriya, Amurka, Afrika ta Kudu, Ghana, Namibia da kuma Jamus - waɗanda suka bayar da labaran irin cin zarafi na lalata da suka fuskanta ko kuma suka gani.

"Ba zan iya ci gaba da jurewa ba. Akwai wata rana da na tashi kai-tsaye zuwa ofishinsa. Na yi magana da karfi: 'Me ya sa kake yin haka? Me ya sa kake cin zarafin duka waɗannan mata?'

"Na daina jin tsoron wannan mutum kowane iri. Ya kura min ido, amma ni ma na yi ta kallon har cikin kwayar idonsa," in ji ta.

Emmanuel, wanda shi ma ya kasance mamban cocin na tsawon shekara 21 da kuma ya shafe gomman shekaru yana zaune a cikin cocin, ya tuno da wannan ranar.

"Shi (TB Joshua) shi ne mutum na farko da ya fara dukanta... daga nan sauran mutane suka bi baya," in ji shi.

"Yana cewa: 'Kana jin abin da take cewa a kaina?' duk da cewa suna ta lakaɗa mata duka, hakan bai hana ta ci gaba da faɗan wannan maganar ba."

Ajoke ta ce an fitar da ita daga cikin ofishin limamin cocin inda aka saka ta cikin wani ɗaki na daban ba tare da sauran mambobin cocin ba, inda ta yi zama ba tare da wani mahaluki ba a wurin har na tsawon shekara ɗaya.

Hakan wani irin horo ne da cocin ke yi wanda ake kira "adaba", abu da ita ma Rae ta fuskanta na shekara biyu.

A wannan lokaci Ajoke ta ce an yi ta bugunta da sarkoki da kuma belt, kusan a kowace rana.

"Na yi mamakin yadda na yi rayuwa a irin wannan yanayi. Na ƙasa tsayuwa da kafafuna na tsawon kwanaki bayan dukan da na sha. Ko wanka ba na iya yi. Yana iya ƙoƙarinsa wajen dakatar da mutane daga saurarona."

Wata rana lokacin da Ajoke take shekara 19, ta ce an rakata zuwa kofar cocin inda daga nan ta fice. An faɗa wa jami'an tsaron cocin waɗanda ke rike da makamai, cewa kada su sake barinta ta koma cikin majami'ar. Wannan ya faru ne shekara shida kafin mahaifinta ya rasu.

"Na koma kwana a waje. Ba ni da wanda zan kai wa kukana. Babu wanda zai yarda da ni. Ban shiryawa irin rayuwar ba," in ji ta.

A matsayinta na matashiya wadda ba ta da kuɗi, Ajoke ta riƙa yin ƴan abubuwan da za ta samu don yin rayuwa, ta kuma shafe shekaru da dama a kan titi.

Ta fara tuntuɓar BBC a 2019 bayan kallon shirin Sashen Binciken Kwaf wanda ya yi wata bankaɗa. Daga nan ta fara wani dogon bincike da BBC domin bankaɗo cin zarafi a cocin na Scoan.

BBC ta tuntuɓi cocin tare da gabatar da zarge-zargen da ke cikin wannan bincike. Majami'ar ba ta mayar da martani ba, sai dai ta musanta zargi da aka yi a baya kan TB Joshua.

"Yin zargi mara tushe kan jagoranmu TB Joshua ba sabon abu bane...Babu wata hujja da aka taɓa gabatarwa a kan haka," in ji cocin.

Da taimakon tsoffin mukarraban cocin da kuma abokai na kusa, Ajoke ta samu barin kan titi a baya-bayan nan. Amma ta shiga mawuyacin hali inda ta so samun matsalar kwakwalwa.

Duk da irin wahalhalu da ta shiga, ta tsaya tsayin daka wajen ganin ta faɗi gaskiya game da mahaifinta.

"Duk lokacin da aka min duka, yana tuna min cewa akwai matsala a cikin tsarin cocin," in ji ta.

Tsoffin mukarraban cocin sun faɗa wa BBC cewa ganin yadda Ajoke ta fito ta faɗi gaskiya kam wannan mutum, na ɗaya daga cikin dalilan da suka sa suka fara kwakwanton imaninsu a kan TB Joshua.

"Ya ajiye dukkanmu a matsayin bayinsa," in ji Emmaneul.

"Ajoke tana da karfin fuskantarsa. Ina ganinta a matsayin gwarzuwa."

Ajoke ta ce faɗan gaskiya yana da muhimmanci a gare ta: "Na rasa komai, gidana, iyalaina, sai dai a gare ni, ba komai bane tun da na faɗi gaskiya.

"Kuma matsawar ina ci gaba da numfashi, zan kare gaskiya, har karshen rayuwata."

Burinta shi ne wata rana ta koma makaranta don gama karatunta da aka yanke.

Charlie Northcott, Helen Spooner, Maggie Andresen, Yemisi Adegoke da Ines Ward ne suka gudanar da wannan bincike na Sashen Africa Eye.