BBC Hausa of Wednesday, 10 January 2024

Source: BBC

Fifa ta hana Overmars karbar mukami a harkar kwallon kafa a duniya

Marc Overmars Marc Overmars

Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, ta dakatar da Marc Overmars daga karbar mukami a harkar kwallon kafa a duniya.

Wani kwamiti ne mai zaman kansa a harkar tamaula a Netherlands ya dakatar da Overmars shekara biyu a kasar cikin watan Nuwamba.

Wannan hukuncin ya biyo bayan "sakonnin da ba su dace ba" da ya aike wa wasu mata abokan aikinsa a lokacin da yake daraktan kungiyar Ajax.

Overmars mai shekara 50, ya bar aikin da yake yi a Ajax cikin Fabrairun 2022.

Kawo yanzu yana aikin daraktan tsare-tsare a Royal Antwerp ta Belbium.

Overmars ya buga wa Ajax wasa sama da 130 tsakanin 1992 zuwa 1997, wanda ya lashe kofin babbar gasar kasar Netherlands uku da Dutch cup da kuma Champions League.

Daga nan ya koma Arsenal, wanda ya lashe kofin lik biyu a Gunners.

Ya kuma taka leda a Barcelona. Bayan ya yi ritaya, ya dauki shekara 10 a matakin daraktan kwallon kafa a Ajax.