Marasa lafiya a Indiya na rububin zuwa rumfar jiran layi a asibitocin masu cutar daji a Silchar da ke arewa maso gabashin ƙasar.
A ‘yan watanni da suka gabata, cibiyar kula da masu cutar daji ta Cachar Cancer Centre, a jihar Assam ta fuskanci ƙarin tururuwar marasa lafiya daga ƙauyuka masu maƙwabtaka.
Dalili shi ne wani juyi da ya haifar da ragi a farashin magungunan cutar daji.
Asibitin na cikin cibiyoyin kula da masu cutar daji na ƙasar, waɗanda kuma suka haɗe kansu suka sayo magani mai tarin yawa sannan suka rage farashinsa da kashi 85.
Matakin ya yi kama da na mai son zuwa saman da ya taka leda, lamarin da ya ceto ƴan ƙasar matalauta da dama.
Tsadar magunguna da tsawon lokaci wajen samun kula da lafiya na yi wa iyalai ƙarƙaf, wani lokacin ma sukan yanke ƙauna.
Misali, kula da kansar mama da ka iya samuwa a lokuta daba-daban kamar sau 10, sannan zai ci kuɗi fiye da $6,000. A ƙasar da mai matsakaicin albashi ke karɓar ƙasa da $700, kenan hakan ya fi ƙarfin aljihun iyalai da dama.
Baby Nandi, mai shekaru 58 na dakon lokacin da za a yi mata gashin cutar ta daji na gaba a asibitin Cachar Hospital.
A baya tana tafiyar kilomita dubu biyu domin samun maganin kansar mama. Farashin maganin shi kansa ya kai $650 a lokaci guda.
Tana buƙatar a duba ta sau shida. Sakamakon kuɗin jirgin da take biya da wurin zama, iyalanta sun shiga matsin tattalin arziki.
To amma sakamakon sabon tsarin da asibitocin suka fito da shi, magungunan yanzu haka sun wadata a garinta, Silchar, a kan farashi ɗaya bisa uku na abin da take biya a baya.
Mai gidan Baby, Naraya Nandi ya ce "Ba mu da isasshen kuɗi a hannu. Dole na sayar da fili sannan na yi rance daga 'yan uwa domin kai ta zuwa Chennai. Aƙalla yanzu za mu iya biyan maganin a gida."
Rahotanni na nuna cewa a duk shekara ana samun masu kansa kimanin miliyan biyu a India, to sai dai kamfanin da ke bayar da shawarwari kan kansa ya ce akwai yiwuwar masu cutar ka iya ninka hakan har sau kimanin uku.
Mafi yawancin mutane a India dai ya zamar musu dole su biya domin samun kiwon lafiya.
Koda masu insorar lafiya ko kuma waɗanda suke kan tsarin kiwon lafiya na gwamnati, za ka ga ba kasafai ake ɗauke nauyin kula da cutar daji kacokan ba.
Amal Chandra, mamallakiyar wani shago a ƙauyen Assam, yana sane da matsalar. A bara lokacin amfanin katin asibitin lafiyar matarsa ya ƙare tana tsaka da samun kulawa dangane da kansar mama da take fama da ita. Katin da ɗauke da darajar kuɗi har $1,800 domin biyan magani. “Dole na ranto $250 domin biyan ragowar kuɗin maganin kansar,” ya shaida wa BBC.
Amal da mai ɗakinsa yanzu haka sun koma asibitin saboda cutar ta daji ta yi mata kome to sai dai kuma sun samu damar biyan gaba ɗaya kuɗin maganin saboda farashin magungunan kansar da aka zabge.
Babban matsalar da ake fama da masu cutar daji ke fama da ita a India ita ce mafi yawancinsu suna zaune a karkara, a daidai lokacin da kuma asibitocin kula da cutar na birane.
Hakan na nufin marasa lafiyar na karkara kamar Mrs Nandi da iyalanta suna fuskantar ƙarin wahalhalu wajen tafiya mai nisa domin samun kulawa.
Kwararru kan harkar lafiya na cewa samar da maganin kansa a waɗannan wuraren babban ƙalubale ne ga tsarin kiwon lafiyar India.
Asibitin Cachar Hospital wanda shi kaɗi ne irinsa a arewa maso gabashin ƙasar, na ƙoƙarin ganin ya warware irin waɗannan matsaloli.
Asbitin na kula da masu kansa 5,000 a duk shekara sannan yana duba wasu ƙarin mutum 25,000, waɗanda ba su da ƙarfin da za su iya biyan kuɗin maganin cutar ta daji da kuma na tafiyar da za su zuwa asibitocin da ke birane.
Hakan dai na nuni da irin nauyin da ke kan kuɗaden gudanarwa na wannan ƙungiyar inda take fuskantar giɓin fiye da $20,000 a kowane wata.
Dr Ravi Kannan, ƙwararren likitan cutar daji wanda kuma shi ke jagoranci ayyukan asibitin, ya shaida wa BBC cewa shirin samar da farashin magungunan kansa mai rahusa ya taimaka masa wajen sayo ingantattun maguguna da kuma bayar da kulawa ga masu fama da cutar a kyauta.
Shirin ya kuma taimaki asibitoci da ke ƙananan garuruwa su gujewa wasu matsalolin kamar barin mugungunan kansar su ƙare musu.
A baya dai rumbun magunguna a asibitocin da ke garuruwan da ba birane ba na da matsala saboda ƙarancin marasa lafiyar da kuma na kuɗi.
"Yanzu kuma ƙananan asibitoci ba sa buƙatar hawa teburin sulhu. An riga an fayyace farashin kuma hakan ya samar da yunƙurin samar da magungunan ga dukkanin asibitoci," in ji Dr Kannan.
Asibitin Tata Memorial Hospital da ke Mumbai, asibitin kula da masu kansa mafi girma a kasar ne dai ke jagoranci wajen sayen magungunan masu yawa.
Da farko dai akwai jerin magungunan 40 na kansa, da suka shafi kaso 80 na farashin magungunan nasu, da suka rage wa ƙungiyar raɗadin dala miliyan 170.
Nasarar da shirin ya samu ya ja hankalin asibitocin tarayya da na jihohi a fadin ƙasar.
Zango na gaba na samar da magunguna zai faɗaɗa zuwa magungunan cutar ta kansa daga 40 zuwa 100, sannan kuma ana ƙokƙarin faɗaɗa sayen sauran kayan buƙata a asibiti.
To sai dai kawo yanzu shirin bai shigar da wasu marasa lafiyar da ke cutuka na musamman ba.
"Ina tunanin ya kamata kamfanonin magani su fahimci cewa a ƙasa kamar India, idan dai har ba ka rage farashin magani ba, ba za ka samu irin kasuwar da kake nema ba," in ji Dr C S Pramesh, darektan asibitin TMH.
Dr Pramesh ya ƙara da cewa kasancewar kaso 70 na waɗanda suka mutu a duniya sakamakon cutar kansa suna a tsakanin masu ƙarami da matsakaicin samu a ƙasashe irin su India, dole ne a samar da shirye-shirye masu kama da shirin samar da maganin cutar daji mai rahusa saboda hakan zai taimaka wa masu cutar a fadin duniya.