BBC Hausa of Friday, 12 January 2024

Source: BBC

Matsalolin rayuwa ne suke hana Antony ƙoƙari - Ten Hag

Erik ten Hag, kocin Manchester United da dan wasa Antony Erik ten Hag, kocin Manchester United da dan wasa Antony

Kocin Manchester United Eric Ten Hag ya ce abubuwan rayuwa ne suka dabaibaye ɗan wasansa na gefe Antony suka hana shi ƙoƙari.

Dan wasan Brazil ɗin yana fuskantar binciken 'yan sanda bayan zargin da ake yi masa na cin razafi wasu mata uku, duk da cewa ba a kamashi ba ko kuma tuhume shi da zargin da ya musanta ba a Brazil ko Burtaniya.

Cikin wasa 21 da ɗan wasan ya yi bai ci kwallo ba, bai kuma bayar an ci ba a wannan kakar.

"Ina ganin matsalolinsa na bayan fili ne ke hana shi ƙoƙariu," in ji Ten Hag.

"Sun matuƙar tasiri a kan sa, dolensa ya yi ƙoƙarin magance su. Za mu ba shi duk wani taimako domin ya koma matsayinsa na baya."

Antony shi ne ɗan wasa na biyu mafi tsada a United a kakar da aka saye shi tun bayan komawarsa ƙungiyar daga Ajax kan kuɗi fam milyan 82 a watan Satumbar 2022, ina ya ci kwallo 24 a wasa 82 da ya buga a gasar Dutch.

Ya ci kwallo 10 ya bayar da biyar an ci a wasa 47 da ya budawa Red Devils a 2022-23 kuma an fara wasa hudu da shi a wasannin wannan shekarar.

A yayin hutun da aka yi na wasan ƙasashe a watan Satumba, kafar yaɗa labarai ta OUL da ke Brazil sun wallafa zargin da tsohuwar budurwarsa Gabriela Cavallin ta yi na zargin cin zarafinta, sai dai Antony ya musanta zargin.

Sauran zarge-zargen sun haɗa da na Rayssa de Freitas da kuma Ingrid Lana waɗanda suka ce ya ci zarafinsu a 2022, shi ma ya sake musantawa.

United ta ce ta ɗauki zargin da muhimmanci, ta hanyar bai wa Antony dama ya tsaya a Brazil a watan Satumba ya kashe wannan matsala sannan kuma za ta riƙa biyan shi albashinsa.

Ya koma atisaye a ranar 29 ga watan na Satumba inda ya tattauna da 'yan sanda Manchester sannan ya koma wasa a farkon watan Oktoba

"A shekarar farko ai ya yi abin kirki, haka lokacin da ake wasanni share fagen fara kaka, kazalika wasanni hudu na farkon wannan kakar," in ji Ten Hag.

"Amma tun daga nan kuma abubuwa suka taɓarɓare masa, ƙoƙarinsa ya ragu ba ya iya abin da ake tsammani.

"Abubuwan da ya riƙa yi a Ajax na birgewa ne kuma muna sa ran zai dawo kansu a yanzu.

"Ba shakka Premeir ya fi wuya amma na san zai iya duk wuyarsa," in ji Ten Hag.

Ten Hag ya kuma yi wa Jadon Sancho fatan alheri a komawar da ya yi Borussia Dortmund da wasa a matsayin aro a farkon wannan makon.